Miyar taushe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Miyan taushe

Miyar Taushe abinci ne na gargajiya da akeyi a gidajen Arewacin Najeriya.

Yanda ake miyar taushe[gyara sashe | gyara masomin]

Kayan hadin miyan Taushe[gyara sashe | gyara masomin]

Kayan miya

Alaiyahu

Nama

Gyada

Kabewa

Mai (manja ko na gyada)

Maggi Mai dandano

Kayan kanshi irin su Onga da sauransu

Citta da tafarnuwa

Gishiri

Kanwa


Nafarko

A markada ko kuma jajjaga kayan miya. A zuba maggi da gishiri da kanwa kadan.Bayan ya dahu a zuba mai a soya sama sama da manja ko man gyada

Na Biyu

A yanka Kabewa kanana. A wanke nama a hade a Dora a tukunya a zuba gishiri kadan da albasa a rufe ya dahu Amma kar kabewar ta yi laushi lubus

Na Uku

Idan su kabewar suka dahu zasu hada kansu

Na Hudu

Sai a zuba kayan Miyar akan su kabewar a kara ruwa yadda ake so. A zuba gyada nikakkiya koh dakakkiya

Na Biyar

Idan ya tafasa sai a juya a zuba su Maggi da gishiri.

Na shida

Idan komai ya dahu yanda ake so sai a zuba albasa a juya. A tabbatar komai yaji yanda ake bukata. Sai a zuba alaiyahu. A bashi minti kadan kar a rufe ayi nisa dan zai iya konewa ko ya dahu dayawa, sannan A sauke

Na Bakwai

Aci da Tuwon shinkafa, Masara, semovita ko masa koh sinasir ko funkaso


Idan Hakan Zai Dan Baka Wahala Zaka Iya Yin haka[gyara sashe | gyara masomin]

In zaki haɗa miyar taushe zaki wanke ki yanka alaiyahu ki ajiyeshi agefe, sai ki yanka kabewa ki dafata ki mitstsika ta ki ajiyeta agefe.

Zaki zuba kayan miyar ki acikin tukunya kizuba mai (manja aka fi amfani da) kiyita juyawa har sai ya soyu sai kisamu ruwan namanki ( wanda kin Tafasa da Albasa ko kayan kamshi irin su tafarnuwa da citta) ki zuba ki tsaida ruwan miyar kizuba kabewar ki kijajjaga da albasa da attarugu .

ki zuba kisa maggi da spices dinki masu dadin d’andano sai ki rufe su, dawo in sun dahu sai ki zuba alayyahun ki kisaka namanki ki rufe in miyar tayi sai ki sauke.

Amfanin Miyar Taushe[gyara sashe | gyara masomin]

Miyan taushe tawa ce mai dadi kuma mai gina jiki da Hausawa ke ci. Wannan hade da kabewa tare da gyada, koren ganye, kayan yaji, da nama yana da dadi, tare da ma'auni mai kyau na yaji da kirim mai tsami, yana sa shi jin dadi. Ana kuma kiranta da miyar kabewa ta Hausa ko miyar kabewa ta Najeriya. Miyan taushe na daya daga cikin miyayan da suka fi shahara a Arewacin Najeriya, tare da miyan kuka (miyan ganyen baobab) da miyan gyada (miyar gyada).

Yawancin lokaci ana ba da shi da masa/waina (cake shinkafa) ko tuwo shinkafa (ballan shinkafa). Koyaya, yana tafiya da kyau tare da yawancin hadiye. Swallow yana nufin ɗanɗano mai kauri, yawanci ana samarwa daga hatsi mai sitaci ko tushen amfanin gona; kuma ana ci da miya a yammacin Afirka.