Muhimmancin Tsaftace Muhalli

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Muhimmancin Tsaftace Muhalli[gyara sashe | gyara masomin]

Muhalli waje ne da al'umma da dabbobi da tsirrai ke rayuwa. A 'yan shekarun nan muhalli na fuskantar kalubale babba daga dumamar yanayi.[gyara sashe | gyara masomin]

Muhalli wani suna ne da ke nufin wurin da ake zama, ko yin wata sana’a da kuma aiki, ya kuma kunshi abubuwa masu yawa da suka sa ake kiran shi haka, sun hada da gida cikin shi da kewaye wato waje, a cikin za, a samu dakuna, dakin dafa abinci, dakin ajiye kayayyaki, wurin wanka, da dai sauransu. Da kuma akwai buqata ta tsaftace su domin aji dadin amfani dasu kamar yadda ya kamata, tsafta dai ita ce abu mai kyau ga kowani irin addini sai da ita, wato idan an tabbatar da ita, za a iya yin ayyukan ibadu na kowani addinai wadanda suka kamata sai an yi su, sai da ita tsaftar za’a iya tunanin yin su daya bayan daya. Wannan ke nan bayan haka kuma sanin kowa ne sai da lafiya ake iya yin al’amura masu yawa, wurin da ya dace kuma a samarwa lafiya muhalli shi ne inda tsafta ta ke, manufa can ne gidan ta, wanda ya fi dacewa da ita. Sauran dayar kuma, wato dauka kowa ai ya san inda kazanta ta ke can ne kyakkyawan muhallin ta.

Ministocin lafiya[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan ya nuna ke nan ashe abin bana wasa bane shi yasa ma har manyan ma’aikatu biyu ake dasu da kuma ministocinsu, na lafiya da kuma muhalli, muddin aka yi sa’a, suna gabatar da ayyukansu kamar yadda ya kamata , to ai komai sai ya kasance za a yi sha’awa da dadin kallo ke nan, idan kuma aka yi rashin sa’ar suna tafiyar Hawainiya ne, abin sai dai ayi sha’ani wai an cuci nakauye.

Idan mu kadan nisa cikin zuciyarmu muna iya gane cewa kwayoyin cuta sune ke kasancewa musabbabin kamuwa da duk wata cuta babba ko kuma karama, akan kirasu da sunan bakteriya, ko kuma birus, da dai sauran sunaye daban–daban.

Qwayoyin cuta su kananan abubuwa ne, saboda ma kankantar su ba kuma za’a iya ganinsu da kwayar idanu ba, sai an yi amfani da madubin Likita wanda ake kira da suna, a Turance Microscope, daga nan sai a gane ko wadanne iri ne da kuma jinsin da suka fito, suna kuma son muhallan ko wuraren da suke da dauka saboda a can ne zasu samu rayuwa mai kyau.


Shi ya sa duk inda aka samu datti ko kumakazanta, to ana fa kyautata zaton da akwai su wadannan kwayoyin cututtuka ba ma cutadaya ba.


Idan aka duba a wannan hali da muke ciki yadda wasu garuruwa suke cikin kazanta ciki da waje, ya kuma kasance suma al’ummar haka suke, ba maganar dakunan kwanansu ba, ga kuma kayayyakin da suke sawa ko kuma (Sutura) wuraren da ake dafa abinci, su kansu a matsayin su na mutane wasu idan suka wuce ji za’a yi suna buga wani irin warin wanda babu ko dadin ji.


Akwai garuruwa ko kuma nace kauyuka wadanda mutum zai gane ko dai sun san abar da ake kira tsafta, amma kuma su ba wannan abin ya dame su ba, sai ka lura dasu akwai wani abinda yafi damun su, wanda kai kuma, gare ka ba mai muhimmanci bane ko misqala zaratun.

Tun ma akofar gidan za’a fara shan mamaki saboda za’a fara yin karo da wani kwatami inda ruwan wanka, wanke-wanke, har ma da Fitsari kan shiga, daga doyi , wari sai kuma wani hamami, wannan ya nuna kwarai da gaske suna shirin tarbar cutar zazzavin cizon sauro ko kuma wata can daban. Ai dama a ire iren wuraren ne suke yin kwayaye masu yawa, su kyan kyashe su, daga baya kuma su kasance matsala ga al’umma, mutum da hankali, wayo , tunaninshi ya sayar da lafiya ya sayi ciwo kamar dai yadda marigayi Alhaji dan Anace ya ce, a wata waqarshi ta Adodan kwaure.

Wani garin, unguwar, gidan ma ana shiga abubuwan da zasu fara yi wa mutum barka da zuwa farkon shiga cikin, basu wuce a samu kwanonin da ake cin abinci, an bar su gajal hakanan duk kudaje nata kai gwauro da kuma mari akan su, ana kallon wurin dafa abinci (kicin) can kuma ba abin mamaki bane har ma Tukwanen dafa abinci wasu ana iya samun watakila an yi sa’a an zuba masu ruwa, wani gidan ma suna iya yin kwana biyu, har sai ya kai ga sun fara yin wari tukuna, an yi magana lokacin ne kuma za’a dauka, aje a wanke.[1]

Dakunan Kwana[gyara sashe | gyara masomin]

Dakunan kwana su ma ko wannen su idan ba sa’a aka yi ba, ba wani abin mamaki bane, a same su, suna buga warin kazanta, ga dai tulin kayan sawa nan masu yawa, wasu na buqatar wanki, amma ba’a wanke su ba, ana jiran sai wani lokaci a wanke. Wanka shi kuma wani ko wata yana iya daukar kwana daya zuwa biyu bai yi ba, kai wani ko wata suna iya yin kwana ma har uku babu wanka, su kasance cikin dauda kayan da suke sawa ma (sutura) su ma daudar, sai maganar wasu soshe-soshe, kai ana ma iya yin babbar sa’a a samu wanda yake da kwarkwata saboda rashin tsafta har Kirci da kazuwa suma sun samu wurin zama ke nan. Wani ma bai damu ba yana tafiya yana soshe –soshen saboda dauda ta kai ga sa ma shi kaikayi, sai ya sosa tukuna ya samu kwanciyar hankali.


A zo cin abinci wani ko wasu ba da muwarsu ce ba, haka za’a sa hannun mai dauke da daudar soshe- soshen da aka yi, ga kuma ‘yan yatsun hannu ba’ a yanke kunba (akaifa) ba, nan madin da akwai wata ajiyar takwayoyin cutar suka yi, ana kuma sa hannu cikin abincin sai daudar ta jiqa abin ya shiga cikin abincin, a riqa ci ana kaiwa zuwa Baki, daganan sa’a ta samu sai Cikin ya dauka.

To a kwana a tashi watarana sai an samu hakuwa da wata babbar bakuwa mai muhimmanci wato cutar da aka aika ma goron gaiyata, ta kuma zo, bai kuma kamata ace mata ai ba masaukin ta bane.

Bayan kuwa ita ta san can ne ya fi dacewa da ita.

Ruwa wanda ake amfani da shi tabangarori daban daban wasu idan aka ga wurin da suke zuwa suna wanka, wanki, can suke dibar ruwan da suke abinci, sha, kai har ma dabbobinsu can ne suke sha, saboda sun yi rashin sa’a basu da rijiyar burtsatse wadda akalla ruwanta yana dakyau da kuma dandano mai dadi wanda ana iya amfani da shi wurare masu yawa. Ba zan manta ba da akwai wani kauye da Allah ya kai mu mun je yin documentary, a sashen Arewa maso Yamma can ne muka samu labarin saboda rashin rijiyoyin burtsatse waxanda ake dasu suna nesa da gari, mutane kuma na zuwa su yi cincirindo, mutum yana iya kwana da yini kafin ya samu ruwan da zai amfani da shi, shi ya sa al’amarin na wancan kauyen sai dai ace Allah ya sauwake, saboda kuwa kamar yadda suka fada mana akwai dan asalin wannan kauye wanda har ma muqamin shugaban karamar Hukuma ya tava riqewa.

Jami’an duba lafiyar muhalli wadanda suke bi gida-gida suna kula da yadda ake tsafatace shi wadanda aka fi sani da Santarori ko kuma sanitary inspectors, akwai su shekarun baya da suka wuce, saboda wani lokacidan Adam zuma ne sai da wuta ake shan shi, idan ba matsa ma shi ake yi ba, sanin shi ne abin fa shi zai fi amfana da shi amma ba zai yi ba sai an tilasta ma shi. Don haka abin da ya kamata ne Jihohin da basu da wadannan Malaman tsaftar sai, a sake dawowa dasu, domin shi muhallin nan ba, tsaftace shi ake yi ba ,akwai matsala,wadda kuma bakarama ba ce sboda kuwa za’a yi ta zaman cikin muhallin da baya dakyau, daga kamuwa da cuta sai kuma abin da ba, a rasa ba. Idan aka yi la’akari da lokacin da ake da su Malaman tsaftar ba wasu cututtukan da ake dasu, yanzu da ana kulawa da muhalli kamar yadda ya dace ayi. Ita ma kanta gwamnatin idan har ta dawo da Malaman tsaftar masu zuwa suna shiga gida-gida suna tabbatar da ana tsaftace su, ai ba, a ware ma bangaren lafiya makudan kudade kamar yadda ake yi yanzu idan maganar kasafin kudi ta taso.

Kamata ya yi a nuna ba, sani ba sabo wajen maganar tsaftace muhalli, kada a bari kowa yana yin abin da yaga dama, ba maganar wani sassauci. Shekara da shekaru sai maganar yadda zazzavin cizon Sauro yake ke ta kassara mutane da yawa duk shekara, amma an kasa gano bakin tsaren, sai Jaki ake ta duka, amma an manta da cewar ashe Taiki ne yake takura ma shi Jakin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://hausa.leadership.ng/muhimmancin-tsafatace-muhalli/amp/