Mujahid Aliyu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Mujahid Ali (Urdu: مجاہد علی‎; an haife shi 3 Afrilu 1972) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan, daga watan Agusta 2018 zuwa Janairu 2023. A baya ya kasance memba na Majalisar Dokoki ta ƙasa daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018.

Rayuwa ta farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 3 ga watan Afrilun 1972.[1]

Ayyukan siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi takara don kujerar Majalisar lardin Khyber Pakhtunkhwa a matsayin dan takarar Jam'iyyar Jama'ar Pakistan (PPP) daga Mazabar PK-25 (Mardan-III) a Babban zaben Pakistan na 2008 amma bai yi nasara ba. Ya samu kuri'u 7,035 kuma ya rasa kujerar ga dan takarar jam'iyyar Awami National Party (ANP).[2]

An zabi Ali a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin dan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) daga Mazabar NA-11 (Mardan-III) a Babban zaben Pakistan na 2013.[3][4][5] Ya samu ƙuri'u 38,233 kuma ya kayar da dan takarar PPP.[6]

A shekarar 2013 ya yi kira da a saki Mumtaz Qadri wanda ya haifar da cece-kuce.[4][5][7]

An sake zaɓarsa a Majalisar Dokoki ta Kasa a matsayin dan takarar PTI daga mazabar NA-20 (Mardan-I) a Babban zaɓen Pakistan na shekarar 2018. samu kuri'u 78,140 kuma ya ci Gul Nawaz Khan, dan takarar ANP.[8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Detail Information". www.pildat.org. PILDAT. Archived from the original on 25 April 2017. Retrieved 24 April 2017.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  2. "2008 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 5 January 2018. Retrieved 23 February 2018.
  3. "10 MNAs get notices for filing unclear statements". DAWN.COM (in Turanci). 6 January 2017. Archived from the original on 3 March 2017. Retrieved 3 March 2017.
  4. 4.0 4.1 "Salman Taseer's assassin: PTI MNA ruffles feathers, demands Qadri's acquittal - The Express Tribune". The Express Tribune. 21 June 2013. Archived from the original on 3 March 2017. Retrieved 15 March 2017.
  5. 5.0 5.1 "Naya Pakistan?: PTI MNA calls for Mumtaz Qadri's release - The Express Tribune". The Express Tribune. 20 June 2013. Archived from the original on 16 March 2017. Retrieved 15 March 2017.
  6. "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 1 April 2018.
  7. "Dangerous statements - The Express Tribune". tribune.com.pk. Archived from the original on 16 March 2017. Retrieved 16 March 2017.
  8. "NA-20 Result - Election Results 2018 - Mardan 1 - NA-20 Candidates - NA-20 Constituency Details - thenews.com.pk". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 31 July 2018.