Ali Isyaku Danja
An haifi Isyaku Ali Danja tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano a garin Ketawa shekaru 57 da suka gabata a karamar hukumar Gezawa ta Kano. ya halarci makarantar firamare ta Yola Wangara daga 1970 – 1976, GSSS Dambatta daga 1978 – 1881. Tsohon malamin firamare ya halarci Kwalejin Ilimi ta Tarayya Kano inda ya sami Diploma, Advance Diploma da Post Graduate Diploma a ci gaban al'umma a fagen siyasarsa Honorabul Ali Danja an zabe shi a matsayin dan majalisar tarayya a jamhuriya ta uku a shekarar 1992. Daga tsakanin 1999 zuwa 2003, ya zama shugaban zartarwa na karamar hukumar Gezawa. Hon. An sake zaben Danja a matsayin dan majalisar dokokin jihar Kano a shekarar 2007 – 2011 inda ya zama mai kare marasa rinjaye a majalisar. An sake zabe shi a wannan kujera a shekarar 2011 – 2015 kuma ya zama mataimakin shugaban majalisar daga bisani ya zama shugaban majalisar. Ankara zabar Honorabul Isyaku Ali Danja a karo na uku a matsayin dan majalisar dokokin jihar Kano a
shekarar 2015.
Hakama Karo na hudu 2019-2023.