Jump to content

Nono

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Nono (Breast))
Nono
organ type (en) Fassara da class of anatomical entity (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na mammary gland (en) Fassara, region of pectoral part of chest (en) Fassara da particular anatomical entity (en) Fassara
Bangare na thorax (en) Fassara, body (en) Fassara, human body (en) Fassara da sex of humans (en) Fassara
Amfani Shayarwa
Facet of (en) Fassara women's health (en) Fassara
Arterial supply (en) Fassara internal thoracic artery (en) Fassara
Venous drainage (en) Fassara internal thoracic vein (en) Fassara
Model item (en) Fassara male breast (en) Fassara da female breast (en) Fassara
NCI Thesaurus ID (en) Fassara C12971
nono

Nono yana ɗaya daga cikin manyan mashahurai guda biyu waɗanda ke kan babban yankin huhu na ƙwanƙolin firamare. Duka mata da maza suna tasowa nono daga kyallen mahaifa iri ɗaya.

Nonon mata yana dauke dawani sinadari da ake kira mammary gland, wanda aikinsa shine samar da ɓoye madararon nono domin shayarwa.[1]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Nonuwan mace halitta ce wadda ta ƙunshi churin tsoka(muscler tissue), kitse (fats), kananan bututu (ducts) da jijiyoyin jini (veins). Sai dai kitse da jijiyoyi sunfi yawa a cikin sa. Wannan ne ma ya sanya cewa girman nonon mace da laushin sa ya danganta ne da yawan kitsen da yake cikin sa, shi yasa zaku ga wata mace tafi wata girman nono. [2]

Nonuwan mace suna fara girma ne daga lokacin da ta kai mizanin balaga (puberty) wanda yake farawa daga shekara 12 zuwa sama. Nono ya ƙunshi wasu ƙananan jakunkuna dunƙulallu (lobes) kimanin 15 zuwa 20, waɗanda su ne su ke samar wa da kuma adana ruwan nono (breast milk).

  1. "Breast – Definition of breast by Merriam-Webster". merriam-webster.com. Archived from the original on 6 September 2015. Retrieved 21 October 2015.
  2. Lafiyata: Bayanan Kiwon Lafiya a Harshen Turanci da Hausa