Taliyan yara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hoton Taliyar Yara

Taliyan yara alama ce ta noodles nan take da kamfanin Indofood na Indonesiya ke samarwa.[1] Indofood kanta ita ce mafi girma mai samar da noodle a duniya tare da masana'antu 16. Sama da fakiti biliyan 15 na Indomie ana samarwa kowace shekara. Ana kuma fitar da Indomie zuwa kasashe sama da 90 a duniya. Manyan kasuwannin fitar da abinci na Indofood sune Australia, New Zealand, Malaysia, India, Iraq, Papua New Guinea, Hong Kong, East Timor, Jordan, Saudi Arabia, Ghana, China, Canada, United States, United Kingdom, France, Brazil, Spain, Jamus , Najeriya, Rasha, Afirka ta Kudu, Mexico, Ukraine, Taiwan, Masar, Lebanon, Japan, da wasu kasashe da suka rage a Gabas ta Tsakiya, Turai, Afirka, Arewacin Amurka, Latin Amurka, da Acia[1].Ana samar da Indomie musamman a Indonesiya tun lokacin da aka fara gabatar da ita a watan Yuni 1972; Har ila yau, ana samar da Indomie a Najeriya tun 1995. Indomie kuma ta yi fice a Najeriya da sauran kasashen Afirka.[3] al,umma na yawan amfani da ita musamman mata da kana nan yara.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2021-12-19. Retrieved 2023-07-07.