Talk:Shamsuabbaty

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

TAMBAYA TA 2:Yaya ake tabbatar da tsayuwar watan Ramadan?

AMSA: Watan Ramadan yana tabbata ne da zarar an ga jinjirin wata ko watan Sha`abān ya cika kwana talatin. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira  cewa Manzon Allah r ya ce: صُومُوا لِرُؤْيَتِهِ وَأَفْطِرُوا لِرُؤْيَتِهِ فَإِنْ غُبِّيَ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلَاثِينَ Ma’ana: Ku yi azumi domin ganinsa (wato Ramadan), kuma ku sha ruwa domin ganinsa (wato Shawwal). Idan watan ya faku a gare ku (ba ku gan shi ba), to, ku cika Sha`abān kwana talatin .

TAMBAYA TA 2:Yaya ake tabbatar da tsayuwar watan Ramadan?[gyara masomin]

AMSA: Watan Ramadan yana tabbata ne da zarar an ga jinjirin wata ko watan Sha`abān ya cika kwana talatin. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira  cewa Manzon Allah r ya ce: صُومُوا لِرُؤْيَتِهِ وَأَفْطِرُوا لِرُؤْيَتِهِ فَإِنْ غُبِّيَ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلَاثِينَ Ma’ana: Ku yi azumi domin ganinsa (wato Ramadan), kuma ku sha ruwa domin ganinsa (wato Shawwal). Idan watan ya faku a gare ku (ba ku gan shi ba), to, ku cika Sha`abān kwana talatin.

TAMBAYA TA 1: Wane irin albishir Manzon Allah (SAW) yake yi wa al`ummarsa kafin watan Ramadan ya kama?[gyara masomin]

AMSA: Manzon Allah (SAW) ya Kasance yana yi wa al`ummarsa bushara da zuwan Ramadan. Kamar yadda hadisi ya tabbbata daga Abu Huraira  ya ce: na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: إِذَا دَخَلَ رَمَضَانُ فُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ وَغُلِّقَتْ أَبْوَابُ جَهَنَّمَ وَسُلْسِلَتْ الشَّيَاطِينُ Ma’ana: Idan watan Ramadan ya shigo ana bude kofofin rahama da kofofin aljanna, kuma ana rufe kofofin jahannama, kuma ana daure shaidanu. Haka kuma an ruwaito daga Anas Ibn Mālik  ya ce: (Watan) Ramadan ya shigo sai Manzon Allah r ya ce: إن هذا الشهر قد حضركم وفيه ليلة خير من ألف شهر من حرمها فقد حرم الخير كله ولا يحرم خيرها إلا محروم Ma’ana: Hakika wannan wata (na Ramadan) ya halarto muku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin da ke cikinsa) hakika an haramta masa alkhairi dukansa. Kuma babu wanda ake haramta wa alherinsa sai wanda bashi da rabo.

TAMBAYA TA 3: Shin ya halatta a yi amfani da qirgen kalanda ko lissafin taurari wajen tabbatar da watan Ramadan?[gyara masomin]

AMSA:Xaukar azumi bisa dogaro da lissafin kalanda ko lissafin taurari bai halatta ba, domin sabuwar hanya ce wadda aka qirqiro. Kuma dogaro da wannan hanyar bidi’a ne. Saboda Manzon Allah r ya ta`allaqa xaukar azumi da ajiyewa a kan gani na ido ne ba amfani da na`ura ta kimiyya ko ilmin taurari ba. Haka kuma, aikin magabata na qwarai bai tabbatar da halaccin yin hakan ba.