Template:Gasar WPWA Gabatarwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Wiki Sound Audio Speaks Campaign gangami ne na Wikimedia yana mai da hankali kan babbar gudummawar Fayilolin Sauti waɗanda suka cancanci encyclopedic don sauƙin raba ilimi kyauta. An tsara wannan kamfen don samar da fayilolin odiyo masu ilimi kyauta na harsuna daban-daban zuwa cikin Wikimedia Commons da kuma haɗa su cikin sauran aiyukan Wikimedia na Harshe daban-daban, da kuma ƙara yawan fayilolin sauti a cikin Wikimedia Commons da yin amfani da waɗannan fayilolin a cikin ayyukan Wikimedia daban-daban musamman ma ayyukan harshe kamar (Wikipedias da Wikitionaries). Kusan duk shafukan Wikimedia suna buƙatar fayilolin sauti, don haka aka tsara wannan shirin domin samun ainihin masu jin kowanne harshen su samar da sautuka a cikin harsunan su a Wikimedia Commons.