Jump to content

Wikipedia:CheckUser

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Wikipedia:Check user)
Logon CheckUser

A zahiri kowane mai bada gudummuwa a Wikipedia ta Hausa yana buƙatar account (User account) ƙwara ɗaya (1) ne kawai.

Misali idan kayi rajistar account mai suna User:Misali, to babu buƙatar ka ƙara yin rajistar wani account. Amfani da account ɗaya yana da matuƙar muhimmanci domin zai tattara maka duka gudummuwar da kake badawa a wuri guda sannan kuma zai baka damar mu'amala da sauran editoci da masu bada gudummuwa ta hanya mai sauƙi da aminci saboda a kodayaushe aka ga sunanka (username) za'a gane ko da wa ake magana.

Idan kuma ya zama dole sai kun ƙirƙiri wani account to ya zama dole ku rubuta shafin kowane account cewa duk na mutum ɗaya ne. Sannan ya zama wajibi cewa ba zaku yi amfani da accounts ɗinba ta hanyar munafunci da yaudara da zaya nuna cewa kamar mutane ne daban masu account ɗin.

Manta lambobin sirri na accounts

[gyara masomin]

A wani lokaci mutane su kan manta lambobin sirri (password) na account ɗinsu na Wikipedia. Abun da ya dace kayi idan ka manta lambobin sirri na account shine ka nemi a canza ma su da sabbi ta hanyar zuwa shafin Special:PasswordReset da bayar da bayanan da suka dace. Ba dai dai bane ka ƙara ƙirƙirar wani account sannan daga baya idan ka tuno lambobin sirrinka na tsohon account kace zaka ci gaba da amfani da accounts ɗin guda biyu ta hanyar da za'a yi zaton mutane ne daban-daban.

Idan kana da tsohon accounts wanda ka manta password, sai ka tuno lambobin sirrin bayan ka riga ka ƙirƙiri wani acccount, to kuna da zaɓi guda biyu.

  • 1. Zaku iya zabar account ɗaya ku cigaba da bada gudummuwa da shi. Dayan kuma ku sanar da admin cewa baku buƙatar shi, a yi blocking ɗinshi.
  • 2. Za ku iya zuwa shafin kowane account ku rubuta cewa eh lallai duka accounts ɗin na mutum ɗaya ne. Wannan rubutun dole ya kasance akan shafin har abada.

Ku sani cewa, a ko wane yanayi, yaudara ce babba, ku zama kuna da accounts sama da ɗaya, sannan kuna amfani da su ta fuskar da sauran editoci da masu bada gudummuwa ba su san cewa mutum ɗaya ke amfani da accounts ɗin ba.

Amfani da accounts na yaudara

[gyara masomin]

Amfani da accounts fiye da ɗaya wajen wannan ayyukan duk yaudara ne, masu yin haka kuma ba'a buƙatar gudummuwar su a Hausa Wikipedia kuma za'ayi blocking ɗinsu kwata-kwata.

  1. Shiga tattaunawa ta hanyar yaudara da nuna cewa kamar mutane ne daban ke da accounts din
  2. Gyara muƙala (Article) da account fiye da ɗaya domin nuna kamar mutane ne da yawa ke gyara mukalar
  3. Lalata mukaloli da sauran sassan Wikipedia da wani account domin boye ainahin account dinka
  4. Duk wani nau'i na rashin gaskiya ko cin zarafi ko halayya da accounts na ƙarya keyi

Aikin CheckUser

[gyara masomin]

Wikimedia tana da fasahar da aka tanadar da zata iya gano duk accounts ɗin daka ƙirƙira ko kuma kake amfani da su (ko da kana ganin kamar ba za'a iya ganewa ba). Za'a iya gane duk abubuwa da kayi a Hausa Wikipedia ko da ba tare da account ba (baka yi login in ba).

Sunan wannan fasahar CheckUser, kuma akwai ta a nan Hausa Wikipedia domin maganin ɓarna da yaudara.

Ta hanyar amfani da CheckUser, za'a iya gane jerin duk adiresoshin IP, da kuma kalan waya ko komfutar da mai bada gudummuwa (editor) yake amfani da su don gyara Wikipedia ta Hausa tare da jerin duk gyare-gyaren da ya taɓa yi daga adireshin na IP ko an yi login account ko ba'a yi ba.

A duk lokacin da akwai zargi mai ƙarfi na cewa wani editor ko mai bada gudummuwa yana amfani da accounts na ƙarya da yaudara, to lallai za'ayi amfani da CheckUser domin tabbatar da hakan. CheckUser zai iya bada duk accounts daka ƙirƙira da kuma duk gyaran da aka taɓa yi da su. Idan har CheckUser ya tabbatar da gaskiyar munafuncin da yaudara (misali ta hanyar aikata abubuwan da aka lissafa a sashen #Amfani da accounts na yaudara), to bamu da ɓukatar ka a Hausa Wikipedia kuma za'a yi blocking ɗinka tare da duk accounts ɗin na ƙarya.

Idan aka yi blocking dinka ta wannan dalilin, to duk wani account daka ƙara ƙirƙira za'ayi blocking ɗinshi ba tare da wani ɓata lokaci ba. Kuma CheckUser yana da fasahar da zai iya nuna duk wani sabon account da ka ƙirƙira ko da kana tunanin ba za'a iya ganewa ba saboda ka canza komfuta ko waya.