Jump to content

Ɗan Bola

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ɗan Bola' shidai ɗan bola mutum ne kamar kowa sai dai kawai ya runguma sana'ar kwasar bola don samu rufin asiri da kuma tafiyar da al'amuran rayuwar sa na yau da kullum. Sai dai ita sana'ar ba kowa bane yake yinta, duk da cewa yawancin masu yinta matasa ne kuma suna fita ne tun da asubahi (wato bayan an fito daga Sallah Asubah). Kafin hantsi yayi wasu har dawo, wasu kuma za suyi ta kewayawa har wajen ƙarfe 10 ko 11 sannan su komo gida suyi wanka.galibin masu aikin kwasar bola dai ba ita kaɗai bace sana'ar su, sunada wata sana'ar a gefe guda wadda daga zaran sun komo gida sunyi wanka Sa'idu fita wata sana'ar. Masu kwasar bola suna amfani da baro ko kuma kura ta ɗaukar kaya.[1]

Mai kwasar bola
  1. Khalid, Aisha (20 October 2022). "Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63". hausa.legit.ng. Retrieved 29 September 2023.