Jump to content

Ƙofar Ƙaura

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kofar Kaura
Kofar_Kaura_03
Kofar kaura ta katsina

Kofar Kaura tana ɗaya daga cikin kofofin cikin birnin katsina. kofar tana akan babban titin da ke hanyar kano.

Asali sunan

[gyara sashe | gyara masomin]

a samu wannan suna ne daga sunan Ƙauran Katsina, wanda sarauta ce ta jarumin mutumin da ke jagorantar rundunar yaƙi. Wannan ƙofa an yi ta ne a kusa da gidan Ƙauran Katsina take. Saboda haka sai ake kiran wannan ƙofa da sunan Ƙofar Ƙaura[1]

Tarihi ya nuna cewa kofar ta samo asali ne daga wani mutum da ake kira da Kaura Gumari, wanda Habe ne, kuma mayaki ne. Ya zauna tare da iyalansa a Garama da ke nan kusa da kofar kaura.

Tarihi ya nuna cewa, wasu daga cikin ‘yan’uwan wannan mutun sun yi kaura zuwa wani gare da ake kira da Tasawa wanda yanzu ke Kasar Nijar, wasu kuma suka yi kaura zuwa tsafe a inda suka kafa mulkinsu a can wuraren. Amma, a wani gurin tarihi ya nuna cewa, kofar Kaura, ta sami sunanta ne a dalilin Kaura Abubakar, wanda ya yi yake-yake a lokacin mulkin Dallazawa saboda kwazon wannan jarumi ne aka ba shi mulkin kula da garin Rimi da ke gabacin da jihar Katsina.

Kuma ta wannan kofar ce, shi Kaura Abubakar ke bi ya fita zuwa Rimi ta nan ne kuma yake dawowa inya fita.

  1. Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.