Jump to content

Ƙofofin gari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ƙofofin gari

Ƙofar gari gini ne da ake yin da ƙasa domin kare kai daga abokan gaba. Ana gina ganuwa ne mai tsayi da faɗi da kuma kauri, daga tsakiya kuma sai a sanya ƙyaren da zaa rinƙa buɗewa ana rufewa.

Akwai masu gadin ƙofa waɗanda su suke kula da ita. Saboda irin yaƙe yaƙen da ake yi wancan lokaci ne yasa ake gina su. Idan abokan gaba suka zo sai su tarar an kulle ƙofa kuma babu hanyar shiga gari. Daga cikin garin ana haƙa kududdufi(ruwa) ta yadda ko da sun hauro to ruwa zasu faɗa duk da cewar tana da tsayin da ba zaa iya hauro ba.

Tarihi Kofar Gadan kaya Kano

[gyara sashe | gyara masomin]

An fara gina ƙofofin gari ne a shekarar 1095 zamanin sarki gijimasu sarkin kano na uku fedrick lugard yayi rubutu akan ƙofofin har ma yace shi bai taɓa ganin wani abu irin wannan ba a Afrika.

Kofar Gadan Kaya - Kano
Sabuwar Kofa kano
Ganuwa or Badala - Kano City Wall - Wajen badalar Sabuwar Kofa
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.