Ƴancin yin magana da dubawa akan cin zarafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ƴancin yin magana da dubawa akan cikin zarafi

Bita akan 'Yancin yin Magana wani bita ne da akayi na tonon silili a cikin al'amarin NHS a Ingila. An sanar da shi a ranar 24 ga watan Yunin Shekarata 2014 kuma Sir Robert Francis ne ya jagoranta.[1] Tun da farko ana sa ran bitar za ta bayar da rahoto a watan Nuwamba shekarar 2014 amma ta dauki lokaci mai tsawo saboda dimbin adadin abubuwan shigarwa a cikin bitar: 17,500 anyi martani kan layi da martanin gidan waya 600.[ana buƙatar hujja]

An buga rahoton a ranar 11 ga Fabrairu, 2015.[2]

Shawarwari[gyara sashe | gyara masomin]

Francis ya zayyana ka'idoji ashirin da ayyuka masu alaqa, sannan ya Kare ta hanyar ba da shawarwari guda biyu kawai:[3]

  1. cewa dukkannin kungiyoyin NHS da masu kula da su da su aiwatar da dukkannin ka'idoji da ayyuka;
  2. cewa Sakatariyar Gwamnati ta rike duba cigaban da ake samu a kowace shekara.

Ka'idoji ashirin don samar da maslaha ga wadannan matsaloli, sa'annan da kuma ba da damar sassauci, sun haɗa da:

  • Al'adar matsaloli masu tasowa - don bada damar yin korafi ga kowanne tsayayyen ma'aikacin NHS.
  • Al'adar 'yanci daga muzgunawa- 'yancin yin magana ga ma'aikata ba tare da muzgunawa ba.
  • Horarwa - kowane memba na ma'aikata yana da damar ya sami horo game da tsarin amincewarsu don yin korafi da kai kara da kuma aiwatar da doka.
  • Goyon baya - duk amintattun NHS yakamata su tabbatar da cewa akwai tsayayyen mutum wanda za'a iya kai wa karar wata damuwa a cikin sauƙi kuma ba tare da wata ka'ida ba, "'Yancin Magana da Wakilai" .

A yanzu akwai sama da wakilai 800 akan 'Yancin yin Magana a cikin kungiyoyi sama da 500 na NHS da kungiyoyi masu zaman kansu, kungiyoyin ƙasa da kuma wasu wurare a kasar Ingila.

A tsakanin shekarun 2020-21, an aiwatar da shari'o'i sama 20,000 akan 'Yancin Magana da Wakilai - wanda suka kunshi ma'aikatan jinya da ungozoma sama da 6,000.[4]

A cikin watan Disamban Shekarata 2021, Ma'aikatan Lafiya da Kula da Jama'a ta Burtaniya ta ba da sanarwar shirye-shiryen gano hanyoyin da za a iya gabatar da 'Yancin Faɗakarwa Masu gadi a sashin kula da zamantakewa.[5]

  • Taimakawa don nemo madadin aiki a cikin NHS - inda ma'aikacin da ya tada damuwa ba zai iya, a sakamakon haka, ci gaba da aikin su ba, NHS ya kamata ta taimaka musu su nemi wani aiki na dabam.

Martani[gyara sashe | gyara masomin]

Yawancin masu fafutuka sun yi iƙirarin cewa shawarwarin ba su yi tsauri ba yadda ya kamata. [6][2]

Wakilin Kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ofishin Masu gadi na kasa kuma kungiya ce mai zaman kanta, wacce ba ta doka ba tare da sadaukarwa don jagorantar canjin al'adu a cikin NHS, ta yadda yin magana ya zama "kasuwanci kamar yadda aka saba". Hukumar Kula da Ingancin Kulawa ne ke daukar nauyin ofishin, NHS Ingila da Inganta NHS.[7]

A cikin watan Janairun shekarata 2016 an nada Eileen Sills a matsayin Wakilin 'Yanci na Farko don Magana kuma Ma'ajin Kasa na NHS.[8][9][10] Ta yi murabus bayan watanni biyu, saboda ba ta da isasshen lokacin da za ta iya hada wannan aiki da sauran ayyukanta. [11]

Dr Hughes ya yi murabus bayan shekaru biyar yana aiki a watan Satumba shekarata 2021.[12]

An rantsar da Dr Jayne Chidgey-Clark a matsayin Mai Tsaron Ƙasa ta uku don 'Yancin Yin Magana akan 11 ga Nuwamba shekarata 2021.[13]

Duba wasu abubuwan[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Freedom to Speak Up Review". webarchive.nationalarchives.gov.uk. Archived from the original on 2015-02-18.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  2. 2.0 2.1 Campbell, Denis (11 February 2015). "NHS whistleblowers report offers no prescription for ending cover-up culture". The Guardian. Retrieved 9 January 2016.
  3. Walsh, Peter (November 2014). "Francis's Freedom to Speak Up review: An openness and transparency revolution or just another report?". Clinical Risk. 20 (6): 128. doi:10.1177/1356262215575958. S2CID 57860342.
  4. Baines, Emma (30 July 2021). "Nurse reports to guardian scheme increased during year of pandemic" – via Nursing Times.
  5. "People at the Heart of Care: adult social care reform". 1 December 2021 – via GOV.UK.
  6. Patrick Sawer, Laura Donnelly The Telegraph (11 February 2015) Whistleblowing: 'It's still not safe for us to speak out'
  7. "Kwafin ajiya". www.nationalguardian.org.uk. Archived from the original on 2019-10-29. Retrieved 2019-10-29.
  8. Dame Eileen Sills Archived 2016-01-26 at the Wayback Machine Care Quality Commission website 7 Jan 2016
  9. CQC appoints first National Guardian for the freedom to speak up in the NHS Care Quality Commission website 7 Jan 2016
  10. The National Freedom to Speak Up Guardian for the NHS Archived 2016-01-26 at the Wayback Machine Care Quality Commission website 7 Jan 2016
  11. Care Quality Commission, New National Guardian appointed to lead the NHS in speaking up freely and safely, 7 July 2016
  12. Discombe, Matt (21 June 2021). "National guardian quits" – via Health Service Journal.
  13. Ford, Steve (12 November 2021). "Nurse chosen to be next 'national guardian' for raising concerns in NHS" – via Nursing Times.

Hanyoyin hahi na waje[gyara sashe | gyara masomin]