AKUYAR SHAMI
Akuyar Shami, asalinta daga ƙasar Syria aka samo ta. Abin da ya sa ta bambanta da sauran awaki shi ne siffar kan ta da girman da take yi. Shiyasa ake kiran mummuna mai kyawun sakamako. Amma Ana kiran Shami da sunaye daban-daban, akwai Shami da Damascene da Aleppo ko Halep ko Baladi.
Wani abun kuma shi ne akuyar na samar da nono mai yawa, da nama da kuma dogon gashi a jikinta wanda a kan sarrafa wajen yin ulun saƙar kayan sa wa.
Binciken ya tabbatar cewa kimanin shekara 70 da ta gabata aka kai wannan akuyar zuwa Cyprus daga Syria domin inganta awakin da ke can, kuma an shafe shekara fiye da 40 ana yin bincike ta hanyar yin aure tsakaninta da sauran nau'in awakin ƙasar. Wannan binciken ya samar da akuya mai bayar da nono da nama mai yawa idan aka kwatanta da sauran awaki.
Siffofin Akuyar Shami
[gyara sashe | gyara masomin]Tana da gashi mai launin ja da ruwan ƙasa, wanda kan yi tsawo sosai. Tana kuma da kunnuwa masu tsawo sosai, waɗanda kan riƙa lilo yayin da take tafiya. Kunnuwan kan kai tsawon inci 12 da rabi.
Bunsurun Shami na da girma sosai, inda nauyinsa kan kai kilo 75, kilo 65 kuma ga akuya.
Shami na da ƙaton kai, inda akan sami bunsuru da akuya na da ƙaho. Amma abin da yafi bambanta ta da sauran awaki shi ne irin fuskar dabbar. Za ka ga tana da banƙararrun fuska da hanci, wanda ke sa wasu su ce mummunar dabba ce.
Tana samar da nono mai yawa, Ta kan samar da nonon da ya kai kilogram 200 zuwa 350 yayin da ta ke shayar da ƴaƴanta, kuma ta kan shafe wata tara zuwa 10 kafin ta yaye ƴaƴanta, ba kamar yawancin awakin yammacin Afirka ba. Ƴaƴan akuyar Shami na balaga tsakanin wata uku zuwa wata 10.
Bunsurun Shami kan kai shekara 12 kafin ya mutu, idan kafin lokacin ba a yanka shi ba. Farashin bunsuru ɗaya ko akuya ɗaya ta Shami kan kama daga dalar Amurka, 1,000 ne zuwa dala, 5,000.
Ana samun Akuyar Shami a ƙasashe Syria da Lebanon da Sudan, da yawanci ƙasashen Gabas ta tsakiya.