Abdoulaye Ousmane

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdoulaye Ousmane
Rayuwa
Haihuwa Maubeuge (en) Fassara, 22 ga Faburairu, 2000 (24 shekaru)
ƙasa Muritaniya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Abdoulaye Ousmane (Larabci: عبد الله عثمان; an haife shi a ranar 22 ga watan Fabrairu 2000) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya a ƙungiyar Lille Reserve ta Faransa. An haife shi a Faransa, yana wakiltar Mauritania a matakin kasa da kasa.[1]

Aikin kulob[gyara sashe | gyara masomin]

Ousmane ya fara wasansa na farko na ƙwararru da kungiyar kwallon kafa ta Strasbourg a cikin rashin nasara da ci 2–0 a Coupe de France a hannun Montpellier a ranar 10 ga watan Fabrairu 2021.[2]

A farkon watan Fabrairu 2022, Ousmane ya koma kulob din Girka Apollon Larissa kan kwantiragin har zuwa Yuni 2023. [3] Duk da haka, ya bar kulob din a watan Yuli.

Daga nan Ousmane ya koma kungiyar Lille ta Faransa a ranar 22 ga watan Satumba 2022. [4]

Ayyukan kasa da kasa[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Faransa, Ousmane dan asalin Mauritaniya ne. Ya buga wasansa na farko a tawagar kasar Mauritania a ranar 26 ga watan Maris 2021 a wasan neman tikitin shiga gasar AFCON 2021 da Morocco.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Abdoulaye Ousmane at FootballDatabase.eu
  2. "Strasbourg vs. Montpellier - Football Match Line- Ups" . ESPN . Retrieved 10 February 2021.
  3. "Ανακοίνωσε μεταγραφές ο Απόλλων Λάρισας!" [Apollon Larissa announced transfers!]. OnLarissa (in Greek). 2 February 2022. Retrieved 23 February 2022.
  4. Bja, Rayan (2 October 2022). "Un nouveau défenseur central rejoint la réserve du LOSC" . Le Petit Lillois (in French). Retrieved 11 October 2022.
  5. "Mauritania v Morocco game report" . Confederation of African Football . 26 March 2021. Retrieved 23 February 2022.