Abdul Rahman Khleifawi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdul Rahman Khleifawi
Rayuwa
Haihuwa Damascus, 1930
ƙasa Siriya
Mutuwa 14 ga Maris, 2009
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da soja
Digiri Janar
Imani
Jam'iyar siyasa Ba'ath Party (en) Fassara

Abdul Rahman Khleifawi: ( Larabci: عبد الرحمن خليفاوي‎, romanized: ʿAbd ar-Raḥmān Khulayfāwiyy - 14 Maris 2009), jami'in sojan Siriya ne kuma ɗan siyasa. Ya kasance Fira Ministan Siriya daga 1971 ya gaji Hafez al-Assad wanda ya zama shugaban Ƙasar Siriya zuwa 1972 na tsawon shekara 1 kuma daga 1976 zuwa 1978 na kimanin shekaru 2, ya zama Firayim Minista na wa'adi biyu tare a karkashin Shugaba Hafez al-Assad.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Khleifawi a shekara ta 1930. [1] Shi ɗan asalin Aljeriya ne, asalinsa daga Draâ Ben Khedda .[2]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Khleifawi babban soja ne. [3] Ya yi aiki sau biyu a matsayin firaministan kasar Syria. Ya fara mulki daga ranar 3 ga Afrilu 1971 zuwa 21 ga Disamba 1972, a matsayin firayim minista na farko a karkashin shugabancin Hafez al-Assad .[3] Khleifawi ya sake zama Firayim Minista daga 7 ga Agusta 1976 zuwa 27 Maris 1978. [1] Ya kuma taba rike mukamin ministan harkokin cikin gida tsakanin shekarar 1970 zuwa 1971 karkashin shugaba Ahmad al-Khatib da firaminista Hafez al-Assad.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Khleifawi ya rasu a ranar 14 ga watan Maris, shekarar 2009.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Syria". World Statesmen. Archived from the original on 17 February 2018. Retrieved 1 January 2011.
  2. "مليون ونصف جزائري بلا هوية مشتتون في المخيمات الفلسطينية". echoroukonline (in Larabci). 19 July 2008. Archived from the original on 26 January 2023. Retrieved 29 July 2018.
  3. 3.0 3.1 Ray Hinnesbusch (2002). Syria: Revolution from Above. Routledge. p. 79. ISBN 978-0-415-28568-1.
  4. "وفاة رئيس الوزراء الأسبق عبد الرحمن خليفاوي". aljaml.com (in Larabci). 15 March 2009. Retrieved 8 August 2023.