Jump to content

Abdulaziz Sani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Marubuci

Abdulaziz Sani Madakin Gini wanda aka fi sani da Yaron Malam (An haifi she a shekarar 1969), a unguwar Gwangwazo dake jihar Kano. Yayi makarantar firamare a makarantar Yelwa daga nan kuma ya hallaci makarantar kimiya da ke a Wudil wato Technical Wudil.

Ya soma harkar rubuce-rubuce a shekarar 1983, wanda rubutunsa ya shafi abin da ya danganci labarai na yaƙi. Littafinsa na farko shi ne ‘Idaniyar Ruwa’ wanda ya wallafa shi a shekarar 1995 daga nan ya rubuta “Duniya Rawar ‘Yanmata da kuma ‘Yaudara Ko Butulci’.

Litttafansa sun yi shura sosai musamman a sanadin ma’aikaci gidan rediyo Muhammad Umar Kaigama.[1]