Jump to content

Abokan Mutum Guda Uku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

MUTUM YANA DA ABOKAI GUDA UKU A RAYUWARSA DA BAYAN MUTUWARSA:

.

1● Abokin da yake tare da kai har numfashinka tun daga ranar da ALLAH ya nufi halittarka har zuwa mutuwarka: shine Arzikinka kuma zai amfaneka har bayan mutuwarka idan kayi amfani dashi ta kyakykyawar hanya musamman Sadaqa mai gudana.

.

2● Abokin da yake tare da kai a yayin rayuwarka da lokacin da ka mutu da bayan mutuwarka: shine ilimin da ka gabatar a lokacin rayuwarka.

.

3●Abokin da yake tare da kai har zuwa Qabarinka inda aka bizne ka da kuma bayan mutuwarka idan ya kasance nagartacce: shine Ɗan ka.

.

Hadith ya tabbata cewa Annabi (ﷺ) Yace: “Idan bawa ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke sai dai abubuwa guda uku:

.

1● Sadaqa mai gudana.

.

2● Da ilimin da ya amfanar.

.

3● Ko kuma Ɗan da ya bari salihi wanda yake masa addu'a.” [Muslim ne ya ruwaito]

.

wannan hadisi yana nuna mana Sadaqa mai gudanarwa ita ce wanda ka taimakawa addininka dashi misalai: ka haƙa rijiya bayin ALLAH suna amfana da ruwan da ke fita daga gareta, ko kuma ka gina masallatai bayin ALLAH suna shiga suna gabatar da ibadah, ko kuma ka gina wata makaranta ta addini, ko kuma ka taimakawa marayu, ko kuma kayi copy na wasu littafan addini mutane suna karantawa suna ƙaruwa da ilimin dake ciki, kaɗan daga ciki ne waɗannan duk sadaqa ce mai gudana.

.

wannan hadisi yana nuna mana cewa idan ka tsaya ka karantar da al'umma wani ilimi da ALLAH ya hore maka shi mutane suka amfana ta dalilin karantarwarka suke maimaita shi, shima ka taimakawa addininka.

.

wannan hadisin yana tabbatar da tsayawa ka bawa yaranka Tarbiyya nagari wanda har zasu samu ikon yi maka addu'a bayan baka raye wannan shima ka taimakawa kanka da kuma addininka domin idan suka zama nagari ana sa ran zasu amfani al'ummah.

.

Waɗannan abubuwa duk ka taimakawa addininka sannan kuma ka taimakawa kanka tunda har bayan ka bar duniya za'a rinƙa rubuta maka ladan, kuma ladan zai rinƙa riskar ka.

.

ALLAH Yasa mu dace (Aameen)

.

Telegram

https://t.me/BINTUSSUNNAH

Facebook

http://www.Facebook.com//Bintusunnah/

YouTube

https://youtube.com/channel/UCG_W7_7gQdibxDgvhQdIEyQ