Abokan wasa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abokan wasa Ba wai ana nufin abokan da muke wasa dasu ba, ko abokanmu na yarinta ko abokan da muke gobza wasa a rukuni ba, Abokan wasa a al'adar bahaushe wasu mutane ne a dangi wanda muka hada wata alaka ta jini dasu ta dalilin iyayen maza ko iyayen mata. A wannan mukala zanyi takaitaccen bayani ne akan wadannan mutane wanda suke a matsayin abokan wasan al'adar Bahaushe.

Su waye abokan wasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ana samun abokan wasa ta bangare biyu,bangaren mahaifi da kuma ɓangaren mahaifiya. Bangaren Mahaifi= ƴaƴan Gwaggonka wato kanwa ko yayar mahaifi sune abokan wasan ka/ki. Bangaren Mahaifiya= Ƴaƴan kawu wato yayu ko kannan mahaifiya sune abokan wasan ka/ki.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]