Jump to content

Abubakar Atiku Rabah Dan Muhammad Bello

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abubakar Atiku Rabah Ibn Muhammad Bello (An haife shi a shekara ta 1873 – 1877). a Wurno, da ne ga Muhammadu Bello kuma jika ga Shehu Usman Danfodio. Abubakar Atiku na rabah shine Kalifa na takwas (8) a cikin jerin kalifofin Sokoto. Ya kuma samu sunan na Rabah ne don shine Mai Garin Rabah kafin zamanshi Kalifa. Yayi karatu mai yawa kuma yana da halaye mai kyau, an yabe shi da gaskiya, adalci da kuma doriya akan ayyukan magabatansa.[1]

Ya kuma fara karatunshi a gida, mafi yawancin malamanshi jinin shine, ma’ana danginshi. Wa inda suke ƙarƙashin mahaifinsa da kuma yan’uwan masu kusanci. Yayi karatun sane a cikin Sokoto da Wurno bayan kammala kananun karatu sai ya fara iya karanta bayan nan kuma aka dogar dashi wajen haddace Al-Qur’ani Mai Girma. Inda daganan ya wuce ya fara su, Fighu, Tauhid and Hadith.[1]

Bayan rasuwar Kalifa Ahmed Rufa’i dan yayanshi Abubakar Ibn Muhammad Bello ya zama sarki a ranar Asabar da safiya mayu (March) 18, 1873. Ya kasance mai girma saboda gaskiyarsa. Har bayan sarautar sa ya kasance yana noma kuma yana ciyar da ahalinsa da guminsa. Sauran dukiyar masarauta kuma ana ciyar da talakawa da masu bukata ne a cikin gari.

Ya rasu ranar Laraba 16, March din shekarar 1877, a lokacin yana da shekara 68 a rayuwarsa. An binne shi a kusa da mahaifinsa Muhammad Bello a garin Wurno.[1]

  • Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.
  • Smaldone, Joseph P. (1977). Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710
  • The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
  1. 1.0 1.1 1.2 Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN p.p 105-118 978-978-956-924-3.