Jump to content

Abubakar as-siddiq

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

==Abubakar as-siddiq GABATARWA Abubakar as-siddiq yana daya daga cikin halifofi shiryayyu, shine na farkon da yafara amsar musulunci acikin maza.

KHALIFANCIN ABUBAKAR AS-SIDDIQ ALLAH YAKARA YARRDA DASHI _Dangan takarsa shine Abdullahi dan abu quhafa Dan ãmir sun hadu da manzon Allah a wurin kakansu na shidda shine murra. Anhaifeshi bayan an haifi manzon Allah da shekara biyu da wata hudu. Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya sha hara da saukin rai,da kyautatawa acikin mu'amalar sa,da tausayawa abokan zamansa. Ya shahara da kasuwanci, sae mutane suka sosa saboda amanarsa, ya maraita acikin shekaru masu yawa, yakasance abun soyiwa a wurin kuraishawa,yana taimakawa gajiyayyinsu,kuma yabawa fakiransu. TARIHIN ABUBAKAR AS-SIDDIQ BAYAN MUSULUNCI Yakasance abokin manzon (tsira da amincin Allah su tabbata agareshi) tun kafin annabta. Yayin da aka aikosa yakasance wanda yafara yin imani dashi acikin maza. Yakira abokanansa, mutane da yawa sun musulunta a hannun sa. Daga cikinsu akwai: Usman dan affan,zubairu dan awwam,Dalhatu dan ubaidullah. Yakasance yana siyan bayi muminai sae ya yantasu domin neman yardar Allah. Lokacin da manzon Allah yayi ya abo kance shi suka shiga kogo tare dashi,yatafi yana taimakonshi a garin madina,kuma taimakeshi a yakokansa, yakasance yana dauke da tuta a yakin tabuka.

kulasatu nurul yakin fiy siratus sayyidil mursalina littalamizul mudarisul ibtida'iyya ajjuzus salis.