Abubuwan dake warware Musulunci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Masallaci

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma’aikin Allah, da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.[1] Bayan haka: Hakika wannan mukalla tana da matukar falala da daraja da matsayi a zukatan al’ummar musulmi, wannan ko ya kasance ne lura da abinda littafin ya kunsa na wayar da kan al’umma akan tsadar da wannan addini na musulunci yake da shi, domin dukkanin wanda ka ganshi musulmi to zabin Allah ne, sai shi musulmin ya tashi tsaye ya yi riko da wannan addini ya kuma godewa Allah da ya yi mishi dace da kasancewa musulmi.

Islam

Nawaqidhul Islam[gyara sashe | gyara masomin]

Idan akace ‘Nawaqidhul Islam’ ana nufin abubuwan da suke warware musulunci, kenan kamar yadda kasan akwai abubuwa da suke warware alwala, zaka ga mutum da laima a hannunsa amma yace maka zai sake alwala saboda ya san ya aikata daya daga cikin abubuwan da suke warware alwala. Haka kuma akwai abubuwan da suke bata sallah da wanda suke suke bata azumi da kuma masu bata Hajji da abubuwan da suke bata sadaka, to haka nan akwai abubuwan da suke bata musulunci (Allah ya tsare mu).

Anan kamata ya yi mutum ya sansu ba ya yi fada ba, domin mutane sun kasu kashi uku awannan Magana:

(1) Musulunci Bai Warwarewa: Anan akwai mutanen da suke ganin kwata-kwata babu yadda za’a yi ace wai mutum musulincinsa ya warware, wannan Magana kuwa cike take da kuskure, sannan kuma ta rusa ayoyi masu tarin yawa da ingantattun hadisan ma’aikin Allah.[2]

(2) Manyan Laifuka Na Fitarwa: Haka kuma akwai wadanda suke ganin ai da zarar mutum ya aikata babban laifi (Kabeerah) to ya fita daga musulunci, wannan Magana itama makare take da kuskure domin ta sabawa karantarwar Alkur’ani da kuma ingantattun hadisan ma’aikin Allah.

(3) Mutum Na Fita Amma… : Sai Magana ta uku wacce itace ta daidai, wacce take tabbatar da mutum yana fita daga musulunci bayan da yana ciki, sabanin maganar farko, kuma ba kowanne aiki ne da ya yi da ya kafirta ba sabanin Magana ta biyu. Ayoyi da yawa da hadisai masu tarin yawa sun fayyace cewar mutum yana fita daga musulunci bayan da yana ciki (Allah ya sawwake), akan hakane malamai suka wallafa litattafai da babi-babi akan hukunce-hukuncen masu ridda.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://islamhouse.com/read/ha/abubuwan-da-suke-warw-are-musulunci-339832
  2. https://d1.islamhouse.com/data/ha/ih_books/single/ha_ABUBUWAN_DA_SUKE_WARWARE_MUSULUNCi.pdf