Jump to content

Ahmed Abdou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmed Abdou
Prime Minister of Comoros (en) Fassara

27 Disamba 1996 - 9 Satumba 1997
Tadjidine Ben Said Massounde (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Mutsamudu (en) Fassara, 1936
ƙasa Komoros
Mutuwa 28 Nuwamba, 2024
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Rally for Democracy and Renewal (en) Fassara

Ahmed Abdou (an haife shi a shekara ta 1936) ɗan siyasar Comoriya ne. Ya kasance Firayim Minista na Comoros daga 27 Disamba 1996 zuwa 9 Satumba 1997.[1]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Mutsamudu a tsibirin Anjouan. Ya taɓa zama ministan kuɗi a gwamnatin Comoros mai cin gashin kansa a taƙaice a shekarar 1972, sannan kuma daga 1973 har zuwa lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1975. Ya sake zama firaministan fiye da shekaru 20 bayan haka a watan Disamba 1996, aka naɗa shi firaminista na Comoros. A watan Mayun 1997 an yi yunƙurin tsige shi, amma ya tsira daga ƙuri'ar amincewar majalisar da ƙuri'u 38-2. Gwamnati ta shiga cikin babbar matsala a cikin watan Agustan 1997 lokacin da biyu daga cikin tsibiran Comoros, ciki har da mahaifar Abdou tsibirin Anjouan, suka ɓalle daga ƙungiyar,[2] kuma an kori Abdou a watan Satumba 1997 bayan watanni 9 yana mulki.

Political offices
Magabata
{{{before}}}
Prime Minister of the Comoros Magaji
{{{after}}}