Jump to content

Aisha bint Khalfan bin Jameel

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aisha bint Khalfan bin Jameel
minista

Rayuwa
ƙasa Oman
Karatu
Makaranta Sultan Qaboos University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

An nada Sheikha Aisha bint Khalfan bin Jameel al-Sayabiyah a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Masana'antu, Oman a shekara ta alif dubu biyu da ukku 2003.

Rayuwar ta ta farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Khalfan a garin Samail, ƙarami a cikin iyali mai yara goma sha ɗaya. Ta halarci Jami'ar Sultan Qaboos ta samu kammala karatu na da digiri a fannin fasaha a shekarar ta 1995.

Bayan kammala karatunta, Khalfan ta yi aiki a matsayin malama. A watan Maris na shekara ta alif dubu biyu da ukku 2003, Sultan na Oman Qaboos bin Said al Said ya ba da doka da ta nada Khalfan a matsayin shugaban Hukumar Kula da Masana'antu ta Oman. Wannan mukamin ya yi daidai da matsayin minista ba tare da fayil ba kuma saboda haka ana daukar ta a matsayin mace ta farko a matsayin ministan Oman. Tare da wannan dokar, Oman ta zama ƙasa ta farko daga Majalisar hadin gwiwar Gulf da ta sami mata minista.[1]

Khalfan memba ce ta zartarwa ta Ƙungiyar Mata ta Larabawa (AWO) kuma ta jagoranci tawagar Oman a Taron AWO na shekarar alif dubu biyu da shidda 2016 inda aka zabi Oman a matsayin shugaban AWO har zuwa shekara ta alif dubu biyu da tare 2019. Ta kuma yi aiki a Kwamitin Amintattun Jami'ar Nizwa kuma memba ce ta majalisar ministoci ta Kungiyar Mata ta Oman . [2][3]

  1. "Oman appoints first female minister". BBC News. 4 March 2003. Retrieved 17 November 2017.
  2. "Board of Trustees". University of Nizwa. Archived from the original on 28 March 2020. Retrieved 17 November 2017.
  3. "The Leading Characters". Omani Women's Association. Archived from the original on 18 November 2017. Retrieved 17 November 2017.