Jump to content

Akin Adesokan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Akin Adesokan marubuci ne ɗan Najeriya, masani kuma mawallafi wanda ke da sha'awar bincike a al'amurran yau da kullum da suka shafi al'adu da adabin 'Yan cirani, 'Yan asalin Afirka da kuma masu ruwa biyu a tsakanin Amurka a ƙarni na ashirin da na ashirin da ɗaya. A halin yanzu shi mataimakin Farfesa ne na adabin kwatance a Jami'ar Indiana Bloomington . Ya yi tasiri sosai a kan yanayin al'adun Najeriya ta hanyar sharhi, shawarwari, da kuma rubutu.