Jump to content

Aknan Bamenda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Pretty Aknan wanda ainihin sunanta Aknan Bamenda yar wasan Kannywood ce ta Najeriya da ta shahara a fitowarta a fim mai taken' Farin Wata Sha Kalo

An haife ta a shekarar 1998,a kasar Kamaru, makwabciyar kasar Najeriya. Aknan ta yi karatun firamare da sakandare a Kamaru kafin ta ci gaba da kammala karatun ta na gaba.

Burin Aknan Bamenda na zama 'yar wasan kwaikwayo ya fara tun tana kuruciya, ta kasance mai son kallon fina-finan Kannywood a wancan lokacin wanda ya sanya ta kaunaci masana'antar.

Bayan kammala karatunta, Aknan ta koma Najeriya inda ta fara tafiya don shiga masana'antar.

Aknan ta fara rawar rawa, bayan ganawa da Adam A Zango, fitaccen jarumin Kannywood, Furodusa, Darakta, Aknan a karshe ta shiga masana'antar fina -finan Kannywood tare da taimakon Adam Zango wanda ya sanya ta shiga cikin ma'aikatan Fim na Fadar White House.

Fim din ta na farko a matsayin jarumar fim shine Farin Wata Sha Kalo, fim wanda maigidan ta Zango ya rubuta kuma ya bada umarni. Kwarewar wasan kwaikwayo da rawar da Aknan ta taka a fim din ya sanya ta zama shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo a Najeriya a halin yanzu.

Tana da kirkira, hazaka, kuma kyakkyawa. Pretty Aknan tana daya daga cikin jaruman Kannywood da yakamata ku lura dasu a shekarar 2021.

Tun shiga masana'antar, Pretty Aknan ta fito a fina-finan Kannywood sama da 15 tare da Ummi Rahab, Zango, Yusuf Guyson da sauran

A halin yanzu Aknan Bamenda tana dan shekara 23 a duniya. An haife ta a shekarar

1998. Aknan Bamenda Addini

Aknan Bamenda Musulma ce. An haifi kyakkyawar jarumar Kannywood Akan kuma ta girma a gidan Musulunci

[1]

  1. https://www.haskenews.com.ng/2021/09/tarihin-jaruma-aknan-bamenda.html?m=1