Al'adan Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Al'adan Hausa
Marina a Birnin Kano
ado da kwalliya
Kuka miyar hausawa
Sana,a a kasar hausa
sana,ar a kasar Hausawa

Al adun Hausawa ko kuma Al adar bahaushe, sune wasu ɗabi u ko ayyuka da suke aikatasu na yau da kullum waɗanda sun shafi na neman arziki da rufin asiri da kuma na nishadi. Na neman arziki sun haɗa da;

  • Saidafatu
  • Kasuwanci
  • Kiwo
  • Noma
  • Jima
  • Ɗinki
  • Saka
  • Tuka igiya
  • Dukanci. da sauransu

Su kuma na nishadi su ne kamar wake-waken waɗanda akwai na sarauta, na isa, kowa da kowa, akwai kadan daga mawaƙan da sukayi suna irinsu;

  1. Dr.Mammam Shata
  2. Ɗankwairo,
  3. Ali makaho,
  4. Ɗan anace
  5. Sa'adu bori
  6. Ɗan maraya
  7. Sani aliyu dandawo. da sauransu.

Sannan daga cikinna al adu na nishadi akwai wasanni kamarsu;

  • Kokawa
  • Dambe
  • Tashe
  • Langa
  • Ogi ogi
  • Kiɗan gwauro. da sauransu

Ga yara da samari a gurin mata da yammata kuwa akwai;

  • Gada
  • Carafke
  • Tatsuniya
  • Dara. da sauransu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]