Jump to content

Al’adun Hausawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
al'adun hausawa
koko
hawan doki
Wasannin hausawa

Farfesa Tijjani Naniya ya ce Hausawa mutane ne musu tsananin rikon al'adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi da abinci da al'amuran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha'anin mu'amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da sauransu, da kuma al'amuran sana'a ko kasuwanci ko neman ilmi.

kunshi

Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al'ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya sun ari na baki ba.

Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga da wando musamman tsala, da takalmi fade ko kafa-ciki, da hula ƙube, ko dankwara, ko dara.

In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani.

Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa, wato gyale da kallabi da taguwa da 'yan kunne da duwatsun wuya wato tsakiya.

Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da gero ko dawa.

Sai kuma sauran abubuwan haɗawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama da kayan rafi da sauransu.

Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka yawancin al'adunsu da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa duk sun ta'allaka ne da wannan addni.

Haka kuma wajen mu'amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin waɗannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan sha'anin sana'a da kasuwanci da neman ilmi duk a jikin Musulunci suka rataya..[1]

Sana'o'in Hausawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Da can sana'a da kusuwanci da neman ilmi suna bin gado ne, wato kowa yana bin wanda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana'a ya shiga baƙon gari zai je ya sauka a gidan abokan sana'arsa ne. Idan ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana'ar gidansu ne saboda haka kusan kowace sana'a akwai sarkinta da makaɗanta da mawaƙanta, kai har ma da wasu al'adu na masu yinta da suka sha bamban da na sauran jama'a.

Hausawa na da sana'oi da dama na gargajiya da suke yi tun fil azal, suna da tarin yawa, amma ga wasu daga cikinsu.

  • Kasuwaci.
  • Fatauci
  • Saƙa
  • Rini
  • Farauta
  • Jima
  • Noma
  • Kiwo
  • ƙira
  • Sassaƙa
  • Dukanci
  • Gini
  • Rinji ko fawa
  • Wanzanci. [2]
  1. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54267063.amp
  2. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54267063.amp