Jump to content

Alhaji Ahmadu Kurfi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

TARIHIN RAYUWA[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Alhaji Ahmadu Kurfi, Maradin Katsina, Hakimin Kurfi, a shekarar 1931 a garin Kurfi, Mahaifinsa shi ne Maradi Aliyu. A lokacin babu makarantar firamare a Kurfi, don haka mahaifinsa sai ya tura shi Katsina domin shiga makarantar firamare ta tsakiya, inda ya yi shekara uku. Daga nan ya wuce Katsina Middle School, sannan ya wuce Kwalejin Kaduna a shekarar 1947. Daga Kaduna ya koma Zariya a 1949. Ya gama makarantar sakandare a karshen 1950, kuma ya samu aikin koyarwa a gwamnatin Katsina ta lokacin. Ya yi shekara biyu a wurin. Daga nan sai ya zarce zuwa sabuwar kwalejin horar da malamai wadda ake kira Higher Elementary Training Centre; inda ya samu horo na shekaru biyu a wurin. Bayan haka sai aka dauke shi aiki a matsayin malamin makaranta a shekarar 1953, kuma a cikin shekarar 1953 din ne ya samu gurbin karatu ya tafi Ingila karo karatu. Ya yi shekara biyar a can yana karatu, inda ya kammala digiri a fannin tattalin arziki Economics a shekarar 1958.

AIKIN GWAMNATI[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara aikin Gwamnati da Native Authority a matsayin malamin makaranta a shekarar 1951, ya soma aiki da gwamnayin Arewa a shekarar 1958, ya kuma yi ritaya a matsayin babban sakataren dindindin na gwamnatin tarayya a shekarar 1986.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://dailytrust.com/at-91-ive-a-good-memory-eat-like-a-young-man-ahmadu-kurfi/