Alhaji Muhammad Adamu Dankabo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Alhaji Muhammad Adamu Dankabo (An haife shi a ranar 4 ga watan Afrilu a shekara ta 1942 ya rasu a ranar 4 ga watan Afrilu a shekara at 2002) a karamar hukumar Kabo ta jihar Kano.[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Yayi karatun Alƙur'ani a garin Kabo. Sannan ya fara karatun firamare a garin gwarzo daga nan ya samu gurbin karatu a makarantar lardi dake garin Kano.

Marigayi ya halarci makarantar horar da aiki jirgin sama ta FTC Kaduna da ta kwaleji BOC da ke kasar Amurka.[2]

Ya samu shaidar difloma ta harkokin kasuwancin sufuri jiragen sama.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Ya sha gwagwarmaya da dama a fannin aiyukan sa daga cikin gida zuwa ƙasashen ƙetare tun daga matsayin me kula da jirgi har ya zamo mai bada abinci ya kuma kai ga matakin mallakar jirgin kansa da kamfanin sa na Kabo Air.[3]

Shuhura[gyara sashe | gyara masomin]

Jarman Kano Adamu Dankabo ya fito da sunan jihar Kano dama Najeriya baki ɗaya a harkar sufurin jirgin sama, saboda wannan hidima tare da gwagwarmaya wacce Dankabo ya yi, ya sanya marigayi martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya naɗa shi sarautar Jarman Kano na farko a daular fulanin Kano.[4]

Ya kuma ba shi aikin kulawa da sabuwar gundumar ƙaramar hukumar Kabo da aka kirkiro daga gundumar Gwarzo wanna aiki yayi har Allah ya kari kwanansa a ranar 4 ga watan Aprilun shekarar 2002.

Rasuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Marigayi Jarman Kano Alhaji Muhammad Adamu Dankabo ya rasu aranar 4 ga watan Afrilun shekarar 2002 yana da shekara 60. Muhammad Adamu Dankabo ya rasu ya bar iyalin sa da dama.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]