Ali Rabi'u Ali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ali Rabi'u Ali(Daddy)

Jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa Kuma darakta Mai daukan nauyi , furodusa,shike da kamfanin Ali rabu,u Ali (A.K.A.), Dake shirya fim a kanniwud.

Masana antar fim[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Rabi'u Ali jarumi ne daya Dade Yana fim tsawon shekaru ,ya shiga Masana'antar tsawon shekaru Ashirin da hudu,Kuma furodusa ne Kuma darakta ne , yayi kirkira, daukan hoto, tsara labari,gyare gyare,rubuta labari,rakoda.

Ya bama masana'antar fim gudummawa sosai a rayuwar sa yayi shekaru Yana cikin Masana'antar ta kanniwud din a hirar da Akai dashi yace yafi fitowa a fina finan dasuka shafi aure, kusan duk fina finan sa akan aure yafi yinsu ganin matsalan aure Dake ta yawaita a kasar Hausa [1]

  • hayaki
  • halisa
  • Gidan hajiya

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Rabi,'u Ali yace takaicin yadda shugabanni ke tafiyan da talakawa a cikin kasa,yasa ya fito takara, ya shiga siyasa a Karkashin jam'iyyar PRP jarumin yace shi jikan aminu Kano ne Kuma ze jagorancin Al umma kamar yadda kakansa yayi ya fito a matsayin Dan majilisan tarayyar a Karamar hukumar dala Dake kano.[2]

Aure[gyara sashe | gyara masomin]

Jarumin yace yanada aure har Allah ya azurtashi da Yara, yayi aure shekarun baya.

  1. https://hausa.legit.ng/kannywood/1469687-jarumin-kannywood-ali-rabiu-ali-ya-fito-takarar-majalisar-tarayya-a-2023/
  2. https://manhaja.blueprint.ng/takaicin-yadda-ake-shugabantar-alumma-ya-sa-na-fito-takara-a-prp-ali-rabiu-ali/

https://www.dandalinvoa.com/amp/na-fi-mayar-da-hankali-wajan-fina-finan-da-suka-danganci-aure/4350473.html