Almara
Almara
[gyara sashe | gyara masomin]Almara wani nau’i ne na adabin baka na Hausa wanda ke ƙunshe da labarai masu ban mamaki ko abubuwan jarumta, yawanci da nufin nishaɗantarwa ko koyar da darasi. Almara galibi tana amfani da abubuwan ban mamaki, dabbobi masu magana, ko jaruman da ke yin abubuwa masu ƙayatarwa, wanda ya bambanta ta da hikaya da tatsuniya.[1]
Almara, kirkiraren labari ne, ba na gaskiya ba, wanda aka tanadar domin samar da nishadi, koya darasi,wayo,tare da kuma wasa kwakwalwa.. Rabe-raben almara Almara ta kasu kashi uku kamar haka:
- Almara Mai Labari. ita wannan labari ake zuba wa kawai a saurara.
- Almara Mai Matsala. ita ce wacce ake kawo wata matsala a nemi masu sauraro su warware ta. Wato a ce ma "idan kai ne ya za kai?
- Almara Mai kididdiga: ita wannan ana kawo labari mai kididdiga kuma a nemi ka warware lissafin.
Almara tana da alaƙa da tatsuniya, amma ta fi mayar da hankali kan labari mai jan hankali da ban mamaki, yayin da tatsuniya yawanci ke ƙunshe da darasi da abubuwan almara na gargajiya.
Siffofin Almara
[gyara sashe | gyara masomin]- Labari mai jan hankali da ban mamaki
- Yin amfani da abubuwan almara, dabbobi masu magana ko jarumai
- Ƙunsar darasi a wasu lokuta
- Ana bayar da labari a lokuta daban-daban, ba lallai da dare kawai ba
- Yawanci yana nishaɗantar da masu sauraro[2]
Misalan Almara
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu misalan Almara daga adabin Hausa sun haɗa da labarai da ke nuna jarumta, hankali, ko halayen ɗan Adam ta hanyar abubuwan ban mamaki:
- Almarar Kowa Tashi Ta Fishe Shi. Labarin Karuwa, Malami da Maharbi): Wata rana, hanya ta hada Maharbi da Malami da kuma Karuwa. Sai suka iske rafi ya kawo,sai Malami ya ce kowa tashi ta fishe shi. Nan take sai Malamin nan ya Dako buzunsa ya yi addu'a ya hau kan buzu, haye ruwan. Da Maharbi ya ga haka sai ya zaro kwari da baka, ya harba kibiya daya can tsallake ta cake a kasa, sai yai ta kara harbawa suna cakewa a jikin junansu har zuwa tsallaken da suke. Sai ya taka kibiyoyin kamar gada ya tsalaka ya haye. Ita ko Karuwa sai ta dakko jakarta ta zaro kayan kwalliywa, ta shafa hoda, ta sa janbaki da ja-gira, sai ta kalli ruwan nan ta yi mashi murmushi gami da fari. Nan take ruwannan ya dare biyu. Ta sa kafa ita ma ta haye.
- Almarar Idan Kai ne Ya Zakai?:wata rana wani mutum zai je unguwa tare da matar shi da mahaifiyarshi da kuma Mahaifiyar matarshi.suna cikin tafiya cikin daji, sai kishin ruwa ya kamasu, amma sai suka yi sa'a , suka iske rijiya da guga ga gabansu. Sai suka zira guga domin janyo ruwa, amma gugar ba ta kaina. Sai aka kula gyaluluwan matan amma dai guga ba ta kai ba. Da aka rasa abin da za a kara kulawa. Sai babar matar ta rige gugar aka zira da ita amma dai guga ba ta kai ba. Don haka sai aka aka babar mijin ta rike kafar mahaifiyar matar aka kara zura su amma dai ba ta kai ba . Ganin haka sai mijin ya rike kafar mahaifiyar shi, matarsa ta rike masa kafa ta zura. Amma yanzu gugar ta kai ta kuma debo ruwa, kafin a a janyo ruwan sai hannu babar mijin ya yi sanyi ta saki babar matar ta fada cikin rijyar tanjaam!. Sai matar ta ce mai nake ji haka sai mijin ya ce, ai hannun babata ne yai sanyi ta saki babarki ta fada. Sai matar ta ce wa mijin ko ka saki babarka ita ma ta fada In jawo ka mutafi mu yi rayuwar duniya ko Kuma idan ka ki in sake ku duka da kai ku fada.
To wai, idan kaine ya za ke?
- Almarar Labrin Kwartaye biyu da Kaza a Karkashin Gado :
Wata rana, mijin wata mace mai Kwartaye, ya yi tafiya. Sai wani kwartota ya ji labari, ya aiko mata cewar zai zo. Ta ce masa to ya zo. Can wajen dare, sai wani Kwartotan ma ya aiko, ya ce mata zai zo. Ta ce shi ma ya zo. Da dare yi, sai ga kwarto na daya ya zo. Suka shiga daki suna hira. Zuwa can, sai suka ji an buga kofa. Sai suka yi zaton mai gidan ne ya dawo. Sai matar ta ce da kwarton nan, ya shiga karkashin gado. Ya shiga Da ta bude kofa sai ta ga ashe kwarto na biyu ne ya zo, ba mijin ba. Suka zauna suna hira. Zuwa can kuma, sai suka ji an sake buga kofa. Suka Rikice. Sai ta ce shi ma wannan kwarton, ya shiga karkashin gadon. Ya shiga suka zauna tare da kwarto na daya. Da ta bude kofa, sai ta ga ashe mijin ne ya dawo,tafiyar ba ta yi tsawo ba. Suka zauna kan gado suna zance. To, ashe a karkashin gadon nan akwai kaza tana kwanci. Can sai kwarto na daya ya ce wa kwarto na biyu. "Aboki, in tambaye ka mana" ya ce, "menene?" Ya ce z "wai maciji sara yake yi ko cizo?" Sai ya ce,."a'a, ai maciji sara yake yi." Sai kwarton ya ce "Subhanallahi, ya sare ni!" Sai daya kwarton ya ce, "ya sare ka!" Sai kuwa suka yi wuf gaba daya, a tsoracez suka yi sama da gado, da wadanda suke kan gadon. Suka baza a guje,kowa ya tashi cikin tsoro.<def>Dangambo (2008), shafi na 58-58.</ref>
Muhimmancin Almara
[gyara sashe | gyara masomin]Almara na taka muhimmiyar rawa wajen:
- Nishaɗantar da yara da manya
- Koyar da darasi cikin sauƙi da ban sha’awa
- Bayyana halayen ɗan Adam da dabi’un jama’a ta hanyar labari mai ban mamaki
- Samar da kayan koyarwa ga malamai da manazarta