Jump to content

Amfanin Man Habbatussauda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Habbatussauda tana da amfani sosai don manzon Allah (s.a.w) yace nahore ku da habbatussauda, don tana magance kowace irin cuta in banda tsufa ko mutuwa,haka kuma malaman duniya sun tabbatar,da cewa tana maganin[1] kowace irin cuta.

Maganin Ciwon Hanta[gyara sashe | gyara masomin]

Cokali guda na Man Habbatus sauda, Cokali uku na Zuma, Cokali guda na garin ‘bawon rumman, ahadasu waje guda asha. Bayan kuma an sha sai kuma asha kofi[2] guda na Nono (tsala ko Kindirmo) ko kuma Madara Gwangwani guda. In sha Allahu za’a samu lafiya daga chutar Olsa, Basur, da kuma ciwon Hanta.

Hawan Jini[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mai fama da hawan jini, a kullum za ka zuba rabin cokali na man Habbatus- Sauda a ruwan zafi daidai yadda za a iya sha, bayan ya huce kaɗan sai a sha. Sannan a kasance masu yawan amfani da tafarnuwa, a abinci, ko shayi , motsa jikin[3] musamman lokacin da rana ta fara fitowa kafin tayi zafi sosai.

Tari[gyara sashe | gyara masomin]

Rabin cokali na man Habbatus -Sauda za a zuba a cikin kofi daya na shayin kofi (Coffee) za a yi haka sau biyu a rana, sannan ka shafa man Habbatus- Sauda a kirjin ka da kuma gadon bayanka.

Inganta Lafiyar Fata[gyara sashe | gyara masomin]

Habbatus- Sauda za ki samu sai ki hada da man zaitun , sai ki wanke fuskar , wannan hadin za ki shafa a fuska , bayan awa daya[4] sai ki wanke.

Zubewar Gashin Kai[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mata masu fama da

matsalar zubewar gashi, sai su hada man Habbatus_Sauda da man Zaitun, bayan su tsefe gashin sai su bi layi-layi na gashin suna sa masa man tare da yiwa kan tausa.

Ciwon Kunne[gyara sashe | gyara masomin]

Irin kwayar Habbatus-Sauda za ka gasa shi sama-sama, sannan ka ni ka shi , sai ka sa man Habbatus- sauda rabin cokali, man Zaitun rabin cokali, sai ka hadesu a mazubi mai kyau, sirinji zaka samu sai ka dure wannan hadin maganai aciki, zaka diga akunne sau biyu a rana.

zafin Jiki[gyara sashe | gyara masomin]

Aduk sanda ka samu kanka a cikin yanayi na zafin jiki, sai ka zuba rabin cokali na man Habbatus-Sauda a cikin shayi mara madara, sai ka sha. Zaka iya cigaba dayi har sai zafin jikin yayi sanyi.

Kurajen Fuska[gyara sashe | gyara masomin]

Ga masu fama da matsalolin kurajen fuska sai ki samu abarba ki markadata sannan ki tace ruwan abarba a kofi, sai ki dauko man Habbatus-Sauda ki sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda, in kuma baki da abarba sai kiyi amfani da lemun tsami mai manya-manya a maimakon abarba. Za ki sha kafin kici abinci da kuma da daddare kafin ki kwanta barci har na tsawon wata 1, sannan za ki iya amfani (Kalonji pimple cream) na fuska. Yana da kyau ki daina cin abincin da zafi sosai. Wandanna sune akdan daga cikin amfani ko tasirin Mai da kwayar irin Habbatus-Sauda ke samarwa ga lafiyar jikinmu. Amma abinda hankulan mu anan shi ne , in kazo siyan man Hbbatus-Sauda ko irin yana da kyau ka kula sosai , don wasu ana siyar masu da “ black caraway” amatsayin Man Habbatus-Sauda wanda kowanen su abu ne mabambanta. Sannan yana da kyau ka kula da iya adadin da za kayi amfani da shi , domin amfanin da shi har yar zarta, ma’ana ya wuce misali na iya illatar da kai. Man Habbatus-Sauda, ana kiran sa da suna daban- daban, aduk inda ka ga an rubuta suna kamar haka “ Kalonji, Black cumin, Habal-al-baraka.” To shi ne black seed oil wato Habbatus-Sauda. Lafiyarka jarinka.

Mura Da Sanyi[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mai fama da mura sai ya samu zuma su hada da Man Habbatus-Sauda, sai ya sha rabin cokali a kullum sannan su diga man kadan a cikin hanci.

Matsalar da ta Shafi Hanci Da Makogwaro[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mai fama da irin wannan matsalolin, sai ya samu lemun tsami mai kyau, ya matse ruwan a kofi sannan ya zuba ruwan zafi sosai akai, rabin cokali na man habbatus- Sauda, sannan sai ya shaki wannan tiririn ruwan zafin. Haka zai yi sau biyu a rana.

Gurbacewar Ciki[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mai fama da, gurbacewa ciki , sai ya sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda a cikin kofi daya kindirmo daya. Za ka sha sau biya a rana.

Ciwon Baya[gyara sashe | gyara masomin]

Ga amasu fama matsalolin ciwon baya sai su , samu kamar cokali 1-2 na man Habbatus- Sauda sai ya dora akan wuta yayi dan dumi, wannan man zasu shafa a bayan su tare da yiwa wajen tausa , a hankali. Sannan su sha man Habbatus- Sauda, karamin cokali sau uku a rana.

Rage Damuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ga masu fama da yawan damuwa , ko kuma su ji duk sun takura , sai su sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda a shayi ko kuma a kofe ( coffee).

Ciwon Kirji[gyara sashe | gyara masomin]

Ga masu fama da ciwon kirji, sai ya samu, man Habbatus-Sauda ya hada da zuma a waje daya, bayan su hada, sai su shafa a daidai inda yake ciwon tare da lailaya man sosai ta yadda zai ratsa cikin jikin sosai, sannan a sha cokali daya da safe da kuma yamma a kullum.

Tsutsar Ciki[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mai fama da tsutsar ciki, sai ya nika irin kwayar Habbatus-Sauda guda 14 , sai ya hada da rabin karamin cokali na man Habbatus-Sauda tare da rabin- rabi karamin cokali na ruwan kal ( apple cider vinegar) sai a hada da ¼ litar ruwa. In shaa Allahu za’a samu sauki.

Matsalolin Al'ada[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mace mai fama da matsalolin da suka shafi al’ada sai ta samu zuma cokali daya ta zuba a kofin ruwan dumi, sannan ta sa karami cokali na man Habbatus-Sauda, sai ki sha sau biyu a rana, har na tsawon kwana 40

Hasken Fata[gyara sashe | gyara masomin]

Man Habbatus-Sauda na da amfani wajen haskaka fata, ba tare da ya haifar da wata illa ba. Abinda za ki yi, shi ne ki samu gram 50 na Man Habbatus-Sauda da gram 50 na Man Zaitun sai ki hada waje guda, za ki sha karamin cokali daya a kullum kafin cin abincin safe.

Amosarin Gashin Kai[gyara sashe | gyara masomin]

Man Habbatus-Sauda 10 grams za ki hada da 30 grams na man Zaitu sannan ki zuba 30 grams na lalle na gargajiya a ciki, kwabasu za kiyi sannan ki dan dumama shi akan wuta, bayan ya dan huce sai ki shafa wannan kwabin akan, sannan ki sa hular lede bayan minti 15-30 sai ki wanke, za ki iya yin haka sau biyu a sati.

Kuturta (Leprosy)[gyara sashe | gyara masomin]

Ga mai fama da ciwon kuturta sai su matse lemun zaki a kofi daya sannan ya sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda ya juya sosai, za ya sha sau biyu a rana. In shaa Allahu za’a samu waraka.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://darussunnahkt.wordpress.com/2020/04/21/amfanin-man-habbattussauda-da-qwayoyinta-ajikin-dan-adam/
  2. https://www.arewangle.com.ng/2022/04/amfanin-habbatussauda-ga-azzakari.html
  3. https://www.taskarmuu.com/2022/09/ashe-haka-habbatus-sauda-ke-da-matukar.html?m=1
  4. https://www.alummarhausa.com.ng/2020/06/maganin-wasu-cututtuka-da-man-habbatus-sauda-yake-ga-lafiya.html
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.