Jump to content

Amfanin ayaba ga lafiyar jiki da fata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Duk wani abu da Allah Ya samar da shi a doron ƙasa na daga ci ko sha yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar wanda aka yi shi domin su, wato ɗan Adam. Sannan a cikin duk wani tsiro akwai alfanun da yake tare da shi ga jikin ɗan Adam, sannan a cikin sa za a iya samun waraka daga wata cuta.

A wani ɓangare kuwa, ana amfani da kowanne sashe na ayaba wurin haɗa wani magani da zai iya warkar da wata cuta. Idan ki ka dafa iccen ayaba, ya dahu sosai, ana shan ruwan don samun sauƙi daga cutar ƙyanda, ciwon kai da kuma zazzaɓi. Za a so a sha kofi biyu zuwa uku a rana.

Su ma masu ciwon zuciya, ana so su yawaita cin ayaba, domin tana taikamawa matuƙa a tafiyar samun lafiyar zuciyar[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://manhaja.blueprint.ng/amfanin-ayaba-ga-lafiyar-jiki-da-fata/