Jump to content

Amfanin kabewa a jikin Dan Adam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyi da ake amfani da kabewa ga rayuwar al’umma suna da yawan gaske musamman ma ga lafiyar jiki, domin Hausawa na cewa “abincinka maganinka”. To ita kabewa Allah ya yi mata baiwa da yawa da take taimakawa, a jiki dan’adam ya samu ingantacciyar lafiya. Kuma ga ita kabewar ba ta da wuyar samuwa haka ma wajen sarrafata babu wata wuya. Ana miya da ganyen ko ‘ya’yan kabewan. Ga dai wasu daga cikin amfaninta.[1]

Gyaran Fata[gyara sashe | gyara masomin]

tana kare fata daga zafin ranar da ke wa fatar jikin mutum illa ya sa ta yi sumul-sumul. Da haka ne masana kiwon lafiya ke mata kirari da ‘mai maida tsohuwa yarinya’.[2]

Tana taimaka wa masu ciwon cutar sikari[gyara sashe | gyara masomin]

domin tana rage yawan ‘Glucose’ bayannan kuma ta kara masu yawan ‘Insulin’ da jiki ke samarwa.

Tana riga-kafin cutar daji[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar yadda cibiyar bincike a kan cutar daji ta kasar Amurka ta tabbatar da cewar, duk abincin da ya kunshi sinadarin da ake kira ‘betacarotene’ ya na ba jiki kariya daga cutar daji, kuma an tabbatar da cewar kabewa na dauke da wannan sinadarin mai yawa.

Lafiyar zuciya[gyara sashe | gyara masomin]

a cikin kabewa akwai wasu sinadarai

dake rage yawan ‘closteral’ a jikin dan’adam wanda hakan ke taimaka wa zuciya. Amma wannan ya na kunshe ne a cikin su ‘ya’yan kabewa.

Karin sha’awar jima’i[gyara sashe | gyara masomin]

Ƴa’yan kabewa na Kunshe da wani sinadari da ake kira da suna ‘zinc’ wanda masana suka bayyana da cewar ¼ na cikin coffin na kunshe da kasha 17 na abin da mutum ke bukata na wannan sinadari a kullun wanda hakan ke kara sha’awa ga namiji.

Maganin gajiya[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai sinadarin ‘potassium’ wanda ya ke taimakawa wajen wartsakar da gajiya da ake fuskanta wajen aikace-aikacen yau da kullun. Ita kabewa na kunshe da wannan sinadarin.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-28. Retrieved 2023-03-28.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-28. Retrieved 2023-03-28.
  3. https://www.alummarhausa.com.ng/2020/10/amfanin-tumatur-da-kabewa-ga-lafiyar-jikin-dan-adam.html