Amina A Shehu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Amina A Shehu jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood, tayi suna ta shahara ta fito mutane da dama an santa.[1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Amina A Shehu jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood. Tayi kokari sosai domin taga ta Gina kanta a masana'antar. Farko da tazo garin Kano tazo da niyyar fim ne dama tana da wasu Yan uwa a cikin garin kano. Bayan ta gama Karatun sakandiri a garin gusau jihar zamfara ta taho Kano domin ta shiga fim. Ta shigo masana antar fim a shekarar 2018 inda ta daukaka sakamakon fim Mai dogon zango Mai suna " GIDAN DANJA" shi ya haskaka ta a idon duniya. Finafinan da tayi.

  • gidan danja
  • gidan mayo
  • Wata makauniya[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://fimmagazine.com/harkar-fim-ta-sauya-mani-rayuwa-jaruma-amina-a-shehu/
  2. https://www.blueprint.ng/how-film-industry-changed-my-life-amina-a-shehu/