Amina ibrahim shekarau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hajiya Amina ibrahim shekarau (An haife ta ranar 11 ga watan Yuni, shekarar alif 1968) a Durumin Zungura Quarters, jihar Kano.[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Tayi Kurmawa a cikin shekarar alif 1974 zuwa 1980. Inda ta gama ta fara primary a shekarar alif 1980 ta gama a shekarar alif 1985. Inda ta wuce tayi sakandire dinta a shekarar alif 1985 zuwa 1989. Sannan tayi makarantar Unguwan Zoma a Kano, a shekarar 2001 zuwa 2003.[1]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Tayi aiki a matsayin Unguwan Zoma a Asibitin Murtala Muhammad a shekarar alif 1989 zuwa 1994. Tayi kuma aiki a Asabitin Muhammad Abdullahi Wase a Kano. Mata ce ga tsohon Gwamnan Kano Alhaji Ibrahim Shekarau.[1]

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

  • Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 · Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. p.p 118-119 ISBN 978-978-906-469-4.