Asalin hausawa
Hausawa, wani jinsi ne na jama'a da suka samu kansu mafi yawa a yammacin Afrika, mutane ne da suka kafa garuruwa daban-daban, sannan duk garin da suka kafa suna da jagoranci na sarautarsu.
Ba su samu damar haɗa kansu wuri guda ƙarƙashin tuta ɗaya ba, hakan ya sa ake kiran kowanne da sunan garinsu da kuma sunan sarautarsu.
kashi
Abin da ya zo ga tarihi, ƙasar Hausa na da manyan garuruwa guda bakwai wato inda suka fara zama, waɗannan garuruwa sun haɗar da Daura da Gobir da Kano da Katsina da Zazzau da Rano da kuma Birom."
Fitaccen masanin tarihin Hausawa, Farfesa Abdullahi Sa'id da almajiransa kamar Farfesa Mahadi Adamu, sun bayyana cewa "asalin Hausawa sun taho ne daga yankin Arewacin jamhuriyyar Nijar, wajen Agadas a yanzu, lokacin da Hamada ta fara buwaya sai neman waje mai danshi da lema da ruwa ya sa wasunsu suka fara sauya matsuguni" suka rika komawa waɗancan garuruwa da aka lasabta a sama da ke Najeriya.
"Waɗanda suka fara kafa tarihi a cikin Hausawa sune Daurawa da suka bunkasa sai suka janyo hankalin mutane da dama daga mabanbantan wurare ciki harda Larabawa", in ji farfesa Mahadi Adamu.
To masu salon Magana kan ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ko da al'adunsu suka fara cudanya sai kuma sabbin matsaloli suka bijiro, da suka haɗa da yunwa da kuma yake-yake, a nan ne wasunsu suka fara hijira suna kafa wasu garuruwan da kuma sarautunsu, duk inda suka kafa gari sai su naɗa sarautarsu, da dama suna alakanta sarautarsu da ita Daura, amma wasu ba su alakanta ba.
Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya ce "a wani kaulin kuma ana ganin Hausawa sun samo asali ne daga yankin gabashin Afrika, can wajen Habasha, dalili kuwa shi ne al'adun gargajiya irin na wannan wuri sun zama kusan daya da irin na Hausawa, domin kamar yadda Hausawa ke bautawa rana kafin zuwan musulunci haka su ma suke bauta wa rana, sannan kayan da suke sanyawa ma yafe ne kamar Hausawa, kana gidajensu ma na rufin bunu ne kamar yadda na Hausawa suke.
Sannan har yau har gobe akwai irin wadannan Hausawa a Habasha."[1]