Jump to content

Ashiru Nagoma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ashiru Nagoma tsohon furodusa ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood fitaccen darakta Wanda ya dade a masana'antar ana damawa dashi. Shine ya shirya manyan[1] fina finai irin su Tutar so, zakka da bakin ta da sauran su , fitaccen mashirin fina finai ne Wanda ya daukaka daga baya rashin lafiya ta same shi.[2]

Rashin lafiyan sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Rashin lafiyan sa ya samo asali ne tunda ya Saka makuden kudade yayi fina finai guda bakwai ya Saka wata fitacciyar jaruma a cikin fim din Amma saboda abinda ya faru da jarumar na Kaddarar hukumar tace fina finai ta Hana a saki fim din NASA[3] , Wanda hakan ya janyo masa asara babba. Abinda ya sashi yawan damuwa kenan da tunani har ya shafi kwakwalwar sa. Ya kwashe shekaru Yana cikin wannan halin Amma duk da haka Yana zuwa gurin da Yan fim suke. A shekarun baya fitacciyar Mai Bada taimako fauziyya D[4] sulaiman ta dauke shi ta kaishi asibiti .[5]

Takaitaccen Tarihin Sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Cikakken sunan sa shine ashiru, Haifaffen jihar Kano ne Kuma be taba aure ba a Rayuwar sa[6]. Ya Sami lafiya bayan da fauziyya D sulaiman ta kaishi asibiti, bayan yayi jinya aka sallame shi a shekarar 2021. Haifaaffen unguwan wurare ne a Kano shekarar sa 43 a duniya be taba aure ba ya daukaka a masana'antar fim a shekarar 2000 zuwa 2014 yayi suna Kuma babban furodusa ne. Shine furodusa San da yake hada jaruman kanniwud kusan gaba da yansu a fim guda. Fina finan sa

  • Gobe da nisa
  • Tarayya
  • Zakka
  • Hiyana
  • Tutar so
  • Bakin ta
  1. https://fimmagazine.com/an-sallami-ashiru-nagoma-daga-asibiti/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
  3. https://www.blueprint.ng/kannywood-agog-over-ashiru-nagomas-reappearance/
  4. https://labarai.com.ng/tag/ashiru-nagoma/
  5. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55666802
  6. https://aminiya.ng/an-kai-daraktan-kannywood-ashiru-nagoma-asibiti/