Auren Hausawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ire Iren auren Hausawa Aure ya rabu kashi-kashi. Akwai auren soyayya da auren dole/tilas da auren zumunta da auren sadaka da auren ɗiban wuta da auren dangana, sannan da auren gayya da auren ɗiban haushi ko ɗiban takaici da ɗiban tsiwa ko kece raini, da kashin ƙwarnafi, da sauran ire-irensu. duk ana cemasu aure.[1].

Aure[gyara sashe | gyara masomin]

Aure alaƙa ce ta halarcin zaman tare tsakanin namiji da kuma mace. Ana yinsa ne saboda abinda aka haifa ya samu asali da mutunci da kiwon iyaye. Kuma shi ne maganin zina da “ƴaƴa marasa iyaye”. Aure muhimmin abu ne ga al’umma. Sabili da haka akwai hanyoyi ayyanannu na tabbatar dashi.[2] Ko kuma a ce aure alaƙa ce ta halaccin zaman tare tsakanin namiji da mace. Ana yin aure domin abubuwa da dama, daga ciki akwai kariya daga zina da samun nutsuwa da kwanciyar hankali, samawa abin haihuwa (abin da aka haifa wato ɗa ko ‘ya) mutunci, da sauransu.

Neman Aure[gyara sashe | gyara masomin]

Matakan neman aure sune, kyautar da yaro ko iyayensa sukan kai gidansu yarinyar da yaro yake so ya nema. Sabili da haka yakan ba ɗiyar wani abun taɓawa. Ko kuma ya kai kyautar wurin iyayenta, ko wasu waɗanda suke da dangantaka da ita, yadda zata gane cewa ana sonta. Ko kuma akai wani abu mai muhimmanci gidansu, kamar kayan na-gani ina-so bayan waɗannan ake ƙunshewa a ba wata tsohuwa ko wani mutum ya kai, daga nan kuma sai a bashi dama ya riƙa zuwa yana magana da yarinyar a gidansu, ko gidan wani ɗan uwanta makusanci, inda ba a yadda za ayi wata manaƙisa  ko wani abu na assha ba. A nan ne yake zuwa shi ko kuma tare da abokansa su zauna su tattauna tare da yarinyar.[2]

Auren soyayya[gyara sashe | gyara masomin]

shi aure na soyayya aure ne wanda saurayi ke ganin budurwa yace yana sonta da aure, ita kuma sai ta amince masa, iyayenta ma su yarda da maganar, kana sai a zo a yi niyyar daurin aure.[3]

Auren Dole/Tilas[gyara sashe | gyara masomin]

A nan saurayi ya kan ga yariya ne yace yana sonta da aure, amma ita bata amince masa ba. Iyayenta kuma su zartar da hukunci, watau ko suna so, ko suna ƙi. Har ma akan bada yarinya ga wanda yake sa’an mahaifinta ne. Ko kuma sa’an kakanta, alhali kuma bata so, tana da wanda take so, kuma akan nemawa saurayi budurwa ba tare da  yana so ba, saboda wata alaƙa ko yarjejeniya da yake tsakanin iyayensu.[4]

Auren Zumunta[gyara sashe | gyara masomin]

: Wannan aure ne wanda ake nema wa yaro ko yarinya daga cikin dagin uwa ko dangi na uba ba tare da an shawarci yaron ko yarinyar ba. Irin wannan auren, ana yinsa don ƙara danƙon zumunta tsakanin ƴan uwa.[1]

Auren Sadaka[gyara sashe | gyara masomin]

Shi auren sadaka aure ne da ake bayar da yarinya ga wani, saboda neman tubarriki, kamar irin sadakar da ake ba malamai, almajiransu, musamman idan yarinya ta girma bata samu mashinshini da wuri ba. Ana yin auren sadaka don gudun kada ta jawo wa iyayenta abin kunya wani lokaci kuma idan mutum bai sami haihuwa da wuri ba, yakanyi alƙawarin  cewa, zai bada ita sadaka in ya samu, yakan ba wani, yace in ya sami Ana yin auren sadaka don gudun kada ta jawo wa iyayenta abin kunya wani lokaci kuma idan mutum bai sami haihuwa da wuri ba, yakanyi alƙawarin cewa, zai bada ita sadaka yakan ba wani, yace in ya sami ƴa’ har ta rayu zai sadaka da ita.[3]

Aure kisan Wuta[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan auren yana kasancewa bayan miji ya saki mace saki uku, alhali kuwa matan tana son mijinta, shima yana son ta, dole sai ta auri wani mutum, kafin ta samu damar komawa zuwa ga mijinta na farko. To, auren nan da tayi, da ƙudurin cewa zata dawo wurin mijinta na da, wannan shine auren ɗiban wuta ko kashe wuta.[4]

Auren Dangana Sadaka[gyara sashe | gyara masomin]

Mutum ya kan auri matar dake zaune a gidan kanta. Sai ya zamana baza ta iya tasowa tazo gidansa ba, saboda waɗansu dalilai. Hakazalika shima ba zai iya zuwa gidanta ya zauna ba. Sai dai ya riƙa zuwa cen gidanta yana kwana. Irin wannan aure, dalilin da yasa ake kiransa dangana-sanda, saboda mai gida yana dangana sandarsa a bakin ƙofar ɗakinta ne, sannan ya shiga ya kwana.[5]

Auren Gayya[gyara sashe | gyara masomin]

Idan matar mutum ta fita, alhali kuwa yana sonta, ya dai sake ta ne don ta addabe shi, to sai yayi sauri yayi wani aure kafin ya sake ta, ko kafin ta gama idda. Ba don komai zai yi wannan auren ba sai don kawai ya fanshe haushinsa, ko kuma don kada matar ta rigashi yin wani aure.[5].

Auren Diban Haushi[gyara sashe | gyara masomin]

ana kuma kiransa auren ɗiban takaici, ko auren tsiwa, ko na kece raini da kashin ƙwarnafi. Idan matar mutum ta dame shi da fitina, yakan takanas ya auri wata mace mai kyau ko dukiya ko asali ko addini, fiye da wacce take gidansa, ko wacce ya saki, ana yin wannan auren do kawai fanshe haushi ko ɗebe takaici ko don a gusar da wulaƙanci da raini da kuma tsiwa na ba gaira ba dalili.[5]

Kayan Lefe[gyara sashe | gyara masomin]

Lefe dai tufafi ne, kayan shafe-shafe, da takalma, da sauran kayayyakin adon mata, su ɗan kunne, da sarƙar wuya, da tsakin lefe, a haɗa a sa a cikin Kwalla a zamanin da kenan, ko fantimoti, ko akwati, a ba wasu mata sukai gidansu yarinya. Wani lokacin kuma akan tara lefe da yawa na masu so daban daban a ajiye har sa’ar da aka tabbatar da wanda aka ajiye har sa’ar da aka tabbatar da wanda aka ga ya dace ya aureta sa’annan a mayarwa sauran nasu, a basu hakuri da zarar yaji an tabbatar masa sai ya aika da neman sa ranan biki.[6]

Sadaki[gyara sashe | gyara masomin]

kuɗi ne wanda mace take ayyanawa a bisa ƙa’idar aure. Kuɗin da ake iya bayarwa a matsayin sadaki, ya tashi tun daga zumbar goma, watau sule da taro ko kwabo goma sha biyar, har zuwa abinda ya ninninka wannan. A wannan kuɗin yau lissafi ya kama daga kwabo goma sha biyu da rabi.[6]

Waliyyan Aure[gyara sashe | gyara masomin]

: waliyyan aure sune dangi na ma’auran nan biyu, akasari iyaye ne ko WALIYYAN AURE: waliyyan aure sune dangi na ma’auran nan biyu, akasari iyaye ne ko ƴa’ƴa ko ƙanne, waɗanda suke wakiltar sashen yaro da sashen yarinya wajen ɗaurin aure. Baza a ɗaura aure ba sai da su.[6]

Shaidu[gyara sashe | gyara masomin]

Ba a daurin aure a sakaye. Dole sai mutane sun shaida. To, mutanen da suke halartar wajen ɗaurin aure, sune shaidu. Lokacin da za ayi fatiha an faɗa a kunnensu sun saurara ko sunji sun shaida cewa, an bada wance ga wane.[6]

Goro da Kudin Daurin Aure[gyara sashe | gyara masomin]

Goro da kuɗi, waɗanda ake rabawa a wajen ɗaurin auren ana baiwa dukkan waɗanda suka halarta ɗaurin auren ne.  Ana bayar da kuɗin zaure,  da kuɗin liman, da kuɗin tauba, sai da kakanni. Kuma ana fitar da kuɗin maroƙa da na ƙattan gari. Ana raba kuɗin ne yayin da aka taru za a shafa fatiha. Akan aikawa ƴan'uwa da masoya, da kuma abokan arziƙi za a ɗaura auren wane da wance a gidan wane. Saboda haka ana gayyatarsu ran kaza a watan kaza da lokaci kaza.[7]

Zaman Lalle[gyara sashe | gyara masomin]

Amarya takan yi ƴan kwanaki biyu ko fiye da haka tana cikin lalle, ana kaita gida-gida ana yi mata gargaɗi, a ja kunnenta kuma a riƙa koya mata waɗansu abubuwa na addini da yadda ake zamantakewan rayuwa. Kuma ƴan'uwa suna yi mata hidima don ganin damarsu da kuma son ransu, kafin ta koma zuwa gidansu ko gidan wani.[8].

Tarewa[gyara sashe | gyara masomin]

Daga nan kuma sai shirya tarewarta a gidan miji. A ranar tarewa, sai ƴan'uwan miji mata su zo gidansu amarya suna neman a basu matarsu, har su bada wani kuɗi na sayen amaryar, sannan a naɗa wata yarinya amaryar boko, bayan tsofaffi mata sun kai amarya ta gaskiya gidan mijinta. Sai a sa wata yarinya ta zama kamar itace amarya. Har a kaita gidan miji ana ta waƙe-waƙe na addini ko na batsa, saboda gudun wata makida ko makirci ko maƙarƙashiya wanda yakan faru daga wasu[8]

Sayen Baki[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ƴanmata sun watse, sai abokan ango su zo don a sayi bakin amarya, sabida baza ta yi musu magana ba sai an biya. Kuma a nan ne samari sukanyi ta wasa ƙwaƙwalwa da sauran magana kala-kala. Sayen baki yakan kasance da daddare ne, a inda ake sakewa ana darawa da kuma nishaɗi.[8]

Budan Kai[gyara sashe | gyara masomin]

Wani ɗan bulaguro ne wanda amarya take yi zuwa gidansu, bayan kwana hudu, ko biyu, ko kuma ma mako ɗaya, saboda azo ayi mata jeren ɗaki, takanyi wannan ƴar ƙaura don a sami damar yi mata wasu ƴan gyare-gyare, kamar su kitso, da aski da shirye shiryen zama da mijinta.[8].

Jere[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu daga cikin makusantan amarya, sune zasu ɗauki ɗawainiyar gyara ɗakin amarya,  suyi jere, da kafin gado, da ƙawace ɗaki, da yin wasu al’adu kamar kafi (Tsari) ko kuma addu’o’i na gargajiya, saboda fatan samun zaman lafiya da kuma kare kai. A rannan ne akan ja kunnen amarya da barin wasu munanan ɗabi’u da yin kyawawansu da dai nisantar aikata abinda zai kawo rashin jituwa a tsakaninsu.[9]

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

  • Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. ISBN 978-2470-25-2. OCLC 702639483.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p.15 ISBN 978-2470-25-2.
  2. 2.0 2.1 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 8 ISBN 978-2470-25-2.
  3. 3.0 3.1 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 15 ISBN 978-2470-25-2.
  4. 4.0 4.1 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 15 ISBN 978-2470-25-2.
  5. 5.0 5.1 5.2 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 16 ISBN 978-2470-25-2.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 9 ISBN 978-2470-25-2.
  7. Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 10 ISBN 978-2470-25-2.
  8. 8.0 8.1 8.2 8.3 Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 11 ISBN 978-2470-25-2.
  9. Alhassan, Habib. (1980–1982). Zaman hausawa. Zarruk̳, Rabi'u Muhammad. Lagos: Islamic Publications Bureau. p. 15 ISBN 978-2470-25-2.