Jump to content

Ayo Obe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ayo Obe (an haife tane a ranar ashirin da hudu ga watan Mayu, shekara ta alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyar wato 1955) lauya ne na Najeriya, marubuci, mai gabatar da talabijin da rediyo kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam. [1][2]

Rayuwa ta farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Obe a ranar ashirin da hudu ga watan Mayu, shekara ta alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyar wato 1955 a Ƙasar Ingila ga iyaye 'yan Najeriya. Ta halarci Jami'ar Wales . [3]

Obe an san tane da kare haƙƙin bil adama na kasar Najeriya, ƙungiyoyin shari'a da zamantakewa, da kuma ba da shawara ga sake fasalin dimokuradiyya. Ta kasance shugabar kungiyar 'yanci ta jama'a [1] kuma ta ba da shawara domin sabunta nasarar zaben shugaban kasa na Cif MKO Abiola na shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da uku 1993.[4][5] An lissafa ta a matsayin daya daga cikin jarumai na sha biyu ga watan Yuni .[6] An kwace fasfo dinta a watan Maris na shekara ta 1996 yayin da ta bar Najeriya don halartar taron Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a New York sakamakon gwagwarmayarta.[1]

Bayan wa'encan fafutukar, Ta jagoranci kungiyar sa ido kan sauye-sauye wacce ta kasance hadin gwiwar sa ido kan zabe da gina dimokuradiyya na kungiyoyin ba da agaji na kasar Najeriya daga alif dubu daya da dari tara da casa'in 1999 zuwa 2001. Ta kuma wakilci hadin gwiwa daga 2001 zuwa 2006 a Hukumar Kula da 'Yan Sanda (PSC). [1]

Tana aiki a matsayin manajan abokin tarayya wato tare da wani manajan a wani kamfanin lauyoyi na Legas mai suna Ogunsola-Shonibare kuma tana zaune a kan kwamitin kungiyoyin farar hula da dama kamar su Goree Institute da kuma kungiyar tarzoma na kasa da kasa wato International Crisis Group. [1] [2][3]

Daga shekara ta dubu biyu da hudu 2004 zuwa Afrilun shekara ta dubu biyu da takwas wato 2008, Obe ta jagoranci kwamitin gudanarwa na tafiyar dimokuradiyya wato Movement for Democracy na Duniya kuma, ta hanyar rike wannan mukamin, ta yi aiki a kwamitin gudanarwar kungiyar dimokuradiyyar afrka wato African Democracy Forum. Ta shiga cikin aikin Gudanar da Tsaro na Duniya wanda Cibiyar Brookings, Jami'ar New York, da Jami'ar Stanford ke gudanarwa. Ta kuma shiga cikin bangarori a Oslo, Beijing, da kuma taron mata.[7]

Littattafai

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Matsalar Matsala ta Najeriya (2007) [8]
  • Bukatar da Gaskiya a Afirka: Tsarin Jam'iyyun Biyu na Najeriya? (2019)[9]
  • Dangantaka tsakanin Dokar Allah da Dokar Dan Adam: Shari'a da Kundin Tsarin Mulki na Najeriya (2005)

Rayuwa ta mutum

[gyara sashe | gyara masomin]

Ita uwa ce marar aure.[10]

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Ugbodaga, Mary (2021-03-08). "IWD 2021: Celebrating 13 Nigerian women who deserve a place on the naira note". TheCable (in Turanci). Retrieved 2021-05-16. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 "Premium Times names ombudsman board for public oversight of its journalism". Premium Times (in Turanci). 2017-05-03. Retrieved 2021-05-30. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":2" defined multiple times with different content
  3. 3.0 3.1 Oladipo, Bimpe (2019-03-04). "OBE, Mrs. Ayo". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2021-05-30. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  4. "Why Does It Matter That Ayo Obe, Eghosa Osaghae, Femi Falana Are Turning 60+?". Intervention (in Turanci). 2020-05-26. Retrieved 2021-05-30.
  5. Sherlaw, Meave (2016-02-22). "The Lagos power list: 21 people in 21 million". The Guardian (in Turanci). Retrieved 2021-05-30.
  6. Ajeluorou, Anote. "Heroes and villains of June 12". The Guardian (Nigeria) (in Turanci). Retrieved 2021-05-30.
  7. "Ayo Obe". Wise (in Turanci). Retrieved 2023-07-07.
  8. Obe, Ayo (2007). "The Challenging Case of Nigeria". Right to Know: Transparency for an Open World Right to Know: Transparency for an Open World / Ann Florini, Ed., ISBN 9780231141581 (in English): 143–175. doi:10.7312/flor14158-005. OCLC 775218836.CS1 maint: unrecognized language (link)
  9. Obe, Ayo (2019). "Aspirations and Realities in Africa: Nigeria's Emerging Two-Party System?". Journal of Democracy. 30 (3): 109–123. doi:10.1353/jod.2019.0046. ISSN 1086-3214. S2CID 199355128.
  10. Okon-Ekong, Nseobong; Obioha, Vanessa (2016-02-14). "14 Powerful Ladies Who Need Love". This Day.