Bacci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgBacci
biological process (en) Fassara
Lion and lioness sleeping.JPG
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na multicellular organismal process (en) Fassara da hali
Karatun ta somnology (en) Fassara
Yana haddasa sleeping (en) Fassara
Hannun riga da wakefulness (en) Fassara

Bacci Wata ni'ima ce daga cikin ni'imomin Allah mai girma da buwaya, wadda yake azurta bayinsa da ita. Domin kowace halitta indai mai raice tana yin bacci mutane da dabbobi duka.

Shi kuma bacci ya danganta da yadda mutum ya saba ma kansa wani zai iya dauka awanni masu yawa yana bacci wani kuma awwani kadan sun ishe shi. Amma dai Likitoci sunyi bayanin iya adadin da mutum yake bukata, misali. Babban mutum yakan bukatu da bacci daga awa bakwai (7) zuwa takwas (8) (7-8hrs) a cikin awa ishirin da hudu (24hrs). Shi kuma yaro daga awa goma (10) zuwa sha biyu (12) (10-12hrs) a cikin (24hrs)

Menene bacci zan iya cewa bacci shine tafiya hankali da tunani da ji da gani da rashin sani meke gudana a lokacin bacci. A takaice bacci yana nufin hutu. A saboda hakane ma Hausawa ke mashi kirari da bacci kanin mutuwa, kuma haka ne saboda idan mutum yana bacci to bai san wanda yake zuwa ba da dawo. Musamman baccin Yara da wasu daga cikin manya.

yaro Yana bacci

Bacci anayinshi ta nau'ka daban daban kowa kuma da kalan nau'in nashi. Sai dai bacci a Musulunci yana da ka'idojin da idan mutum yabi su yakan samu tsari daga shaidanu da aljanu ya kuma samu Lada daga mahaliccin sa. Annabi Muhammad (S A W) ya koyar damu wasu ladubban bacci ga kadan daga wadanda zan iya kawo wa:

  1. Alwala
  2. Addu'a irin karanta Ayatul Kursiyyu sau daya Falaki da Nasi kafa Uku-uku, in ya gama karanta su sai ya hade hannanyen sa ya tofa sai ya shafe jikin shi duka zai fara daga kai har iya inda hannanyen sa ya kai.
  3. doki Yana sharara bacci
    Kwanciya a ta gefen dama (akan hannu dama) hannun mutum a kuncin sa, hannun dama kenan sai na hagu ya dora shi akan jikin shi. A daidai lokacin akwai kuma wata addu'a da ake so mun yayi (باسمك اللهم أموت وأحيا. اللهم قني عذابك يوم تبعث عبادك) shikenan sai mutum ya fara baccinsa.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]