Bahir Nayaya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

'Bashir Nayaya jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya dade yana fim a masana'antar Yana taka rawa a matsayin UBA a masana'antar. Ya fito a shahararren fim din Nan na Tashar Arewa 24 Mai suna KWANA CASA'IN inda ya fito a suna malam nura baban safara,u, fim din ya Kara haskaka [1]shi a idon duniya.[2]

Takaitaccen Tarihin Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Bashir Nayya jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud an haife shi a ranar 4 ga watan fabrairu shekarar 1968 a jihar Kano. Ya fara fim Yana da shekaru 40 , ya fara a shekarar 2008 tun daga Nan yake aktin a matsayin UBA. Kafin kanniwud shi Dan kasuwa ne Amma Sha,awan sa da masana antar yasa ya shigo ya bar kasuwancin. Farkon fim dinsa shine fim Mai [3]suna"Dijangala" Wanda akayi a shekarar 2008.[4]

Fina finan sa.

  • Dijangala(2008)
  • HUBBI(2012)
  • Dan baba(2009)
  • Gabar cikin Gida(2013)
  • Rai dangin goro(2013)
  • Sarki jatau(2013)
  • Bana bakwai(2008)
  • Yancin(2015)
  • Mijin yarinya[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.bbc.com/hausa/media-57582085
  2. https://www.nollywire.com/names/bashir-nayaya/
  3. https://www.nollywire.com/names/bashir-nayaya/
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
  5. https://networthpost.org/net-worth/bashir-nayaya-net-worth/