Bakace

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Bakace wata hanya ce da ake amfani da ita don tsaftace/rege hatsi daga datti, ana zuba hatsin ne a tire domin a banbance tsakanin hatsin da tsakuwa. Ko kuma bayan an kuma surfa hatsi ko suefen hannu ko na inji, sai azo da kuma mabakaci don tacewa tsakanin hatsin da dusa. Zalla dai mata su aka fi sani da harkar bakace. Akwai kuma kalmar Bakance wadda ita kuma take nufin alwashi, Kamar mutum yace idan Allah ya bani kuɗi tohm zanyi azumi tsawon kwana kaza.[1]

Wata Dattijuwa/Tsohuwa tana bakacen Masara da mabakacin kaba
Mabakacin kaba na Hausawa

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Bakace". hausadictionary.com. Retrieved 27 September 2023.