Jump to content

Big Hit Music

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Big Hit Music
Bayanai
Iri record label (en) Fassara da record production team (en) Fassara
Masana'anta music industry (en) Fassara
Ƙasa Koriya ta Kudu
Mulki
Hedkwata Yongsan District (en) Fassara
Tsari a hukumance ƙaramar kamfani na
Mamallaki HYBE (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1 ga Yuli, 2021
Wanda ya samar

ibighit.com

BigHit music gidan rukodin din wakoki ne na koriya ta kudu, wanda aka kirkira a shekara 2005 wanda Bang Si-hyuk ya kirkira. An sake ginashi tare da qara ingantashi zuwa kamfani mai zaman kanshi, a karkashin Hybe cooperation (wanda a DA akasanshi da bighit Entertainment Co., Ltd) tun shekarar 2013 zuwa yanzu.gidane wanda ya kunshi manyan mawaka kamar guruf din BTS da guruf din TXT.

Big Hit Entertainment Logo

An kafa Big Hit Entertainment a ranar 1 ga Fabrairu, 2005,kuma ya sanya hannu kan muryar sautin 8Eight a cikin 2007.A cikin 2010, kamfanin ya sanya hannu kan kwangilar gudanarwa ta haɗin gwiwa tare da JYP Entertainment akan ƙungiyar maza ta 2AM.A waccan shekarar, Bang Si-hyuk ya rattaba hannu kan RM a matsayin memba na farko na BTS kuma ya kaddamar da taron kasa da kasa don daukar wasu membobin kungiyar—BTS sun fara halarta farko a karkashin big Hit a ranar 13 ga Yuni, 2013. A cikin 2012, kamfanin yayi saynin din Lim Jeong-hee, kuma ya kafa ƙungiyar yara mata "GLAM" a matsayin haɗin gwiwa tare da Source Music. Kungiyar ta kasance tana aiki har zuwa 2014 lokacin da aka wargaza ta saboda wata takaddama da ta shafi daya daga cikin mambobinta, Kim Da-hee,—An yanke wa Kim hukuncin zaman gidan yari bayan da aka same ta da laifin yin lalata da jarumi Lee Byung-hun. Bayan ƙarshen kwantirak na haɗin gwiwa tsakanin Big Hit da JYP a cikin Afrilu 2014, mambobi uku na 2AM sun koma JYP, yayin da Lee Chang-min ya kasance tare da Big Hit don ci gaba da aikinsa shi kadai kuma a matsayin ɓangare na duo Homme.A Shekarar kuma kungiyar 8Eight ta watse bayan kwantirak din "Baek Chan" da "Joo Hee" tare da Big Hit ta ƙare. A watan Mayun 2015, Lim Jeong-hee ta raba hanya da hukumar, bayan karewar kwantiraginta na shekaru uku[1]. A cikin Fabrairun 2018, Homme ya watse bayan kwangilar memba Changmin ta zo ƙarshe. Ya bar kamfanin don kafa tasa hukumar, yayin da Lee Hyun yacigaba da kasancewa mawaki na solo. A watan Oktoba, BTS ta sabunta tare da tsawaita kwangilar su da hukumar har tsawon shekaru bakwai. Big Hit ta fito da guruf na biyu,wato (TXT), a cikin Maris 2019[2]. [3]

Wakar Girls of my Dreams da aka rubuta
  1. Hwang, Hye-jin (June 12, 2013). "Big Hit Reveals Lim Jeong Hee′s Contract Ended in May". Newsen. Archived from the original on December 30, 2015. Retrieved April 3, 2021 – via Mwave.
  2. Kelley, Caitlin (February 6, 2019). "BTS's Label Reveals TOMORROW X TOGETHER Will Debut March 4". Forbes. Archived from the original on February 7, 2019. Retrieved April 3, 2021.
  3. 글램, 결국 3년 만에 해체…'이병헌 협박女' 다희-이지연 실형 선고 [Glam, finally disbanded after three years...'Lee Byung-hun blackmailed' Da-hee & Lee Ji-yeon sentenced to imprisonment]. Sports Chosun (in Korean). January 15, 2015. Archived from the original on August 8, 2016. Retrieved April 3, 2021