Jump to content

Birnin Gozaki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gozaki garin Ɗiya, inba ɗiyan mutum akwai ɗiyan kuka”[1] wanna wani shahararren kirari ne da akewa birnin Gozaki, kuma alamu ne dake nuna cewa gari ne mai albarkatun hutawa da ƴaƴansa masu amfani”[1].

Birnin Gozaki tsohon gari ne mai ɗimbin tarihi wanda ake tunani an gina shi a tsakiyar ƙarni na goma sha biyar (15th century) kuma ga dukkan alamu garin ya samu lokuta biyu na kafawa, dangane da kafuwar garin, masana tarihin garin sunce, wani mutum mai suna “ƙyangaran” ya kafa shi, kuma ya gina ganuwar don kariya da tsoro, wanda shi maharbi ne kuma yazo ta[2].

Abubuwan tarihin da ke cikin tsohon Birnin Gozaki sun haɗa da ganuwa wanda har yanzun akwai alamunsa. Sannan “Rafin ƙofa” “ko asamahen” wanda yayi iyaka da tsohon garin Gozaki da kuma sabon garin.Akwai kuma gidan maharba, da wani kogon dutse da ake ajiye makami. Sannan akwai wani iccen kuka da ake kira “ƴar Barogo” a lokutan da, da zaran a ji guɗa ta fito daga kukar to ansan yaƙi ya kusa zuwa garin, sai mutanen garin su shiga shirin yaƙi. Akwai kuma wata rijiya mai suna “Ɗan Bori” wanda indai aka ji guɗa daga cikinta to lallai mutanen Gozaki za su yi nasara a yaƙin[2].

Har wa yau akwai wani iccen rimi wanda wata ƴar kaza ke fitowa, da zarar ta fito sai a kiyayi wajen idon kuwa ba haka ba, za a mutu ko a sami nakasa[2].

Sannan yanzu haka akwai wani da ake kira da “Bangadifa” da ke rufe da wani baho wanda ance duk ranan da bahon ya buɗe to ruwa zai ci garin Gozaki, hakazalika akwai wani wuri “Gunki” wanda ba hali abi wurin, in ba haka ba za a ga maciji ya fasa kai yana huci.

Sannan garin Gozaki ya shahara a harkar noma musamman noman auduga[3].

Wasu daga cikin sarakunan garin Gozaki da ake iya tunawa sun haɗa da:

Sarakunan Maguzawa

1.    Sarkin Gozaki Katanko

2.    Sarkin Gozaki Agaji

3.    Sarkin Gozaki Tuje

4.    Sarkin Gozaki Gulun

5.    Sarkin Gozaki Maɗa

6.    Sarkin Gozaki Jingi[4]

Sarakunan Haɓe

1.    Sarkin Gozaki Jatau

2.    Sarkin Gozaki haruna

3.    Sarkin Gozaki Usman[5]

 Sarakunan Fulani

1.    Sarkin Fulani mai Gamo

2.    Sarkin Fulani Ɗan Magaji Abdu

3.    Sarkin Fulani Dakara

4.    Sarkin Fulani Muhammadu Bello (1876 - 1897)

5.    Sarkin Fulani Abu (1897 - 1901)

6.     Sarkin Fulani Abdullahi (1901 - 1936)

7.    Sarkin Fulani Mammn Lawan (1936 -1983)

8.     Sarkin Fulani Halliru Lawal (1983)[6].

Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.

  1. 1.0 1.1 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.36. ISBN 978-2105-93-7.
  2. 2.0 2.1 2.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 39. ISBN 978-2105-93-7.
  3. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 39. ISBN 978-2105-93-7.
  4. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 39-40. ISBN 978-2105-93-7.
  5. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 39-40. ISBN 978-2105-93-7.
  6. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Garkuwan Jihar Katsina. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p. 39-40. ISBN 978-2105-93-7.