Blinken antony j. blinken
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Antony John Blinken (an haifeshi 16 ga watan Afrilu, 1962) ya kasance ma'aikacin gwamnatin kasar Amurka ne kuma dan diflomasiyya ne wanda yake aiki tun 26 ga watan Janairu, 2021 a matsayin sakataran Amurka na 71. Yayi aiki a matsayin mataimakin mai bada shawara a kan tsaro na kasa daga 2013 zuwa 2015 da kuma mataimakin sakataran kasa na kasar Amurka daga 2015 zuwa 2017 a karkashin gwamnatin shugaba Barack Obama.
Tarihi da kuma karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haife Blinken a 16 ga watan Afrilu a shekarar 1962, a Yonkers dake jahar New York, iyayenshi Yahudawa ne, Judith (Frehm) da Donald M. Blinken, wanda yayi aiki a matsayin ambasadan Amurka a kasar Hungari. kakanninshi na bangaren uwa Yahudawa ne na kasar Hungari. Kawun Blinken, Alan Blinken yayi aiki a matasayin ambasada na Amurka a kasar Beljiyan. Kakanshi na bangaren uba, Maurice Henry Blinken yana daga cikin magoya bayan Isra'ila na farko-farko wanda ya karanci tattalin arzikinta, kuma kakan kakanshi shine Meir Blinken, marubuci ne na yaren Yiddish.
Blinken yayi karatu a makarantar Dalton dake cikin birnin jahar New York har zuwa 1971. Blinken yayi karatu a jami'ar Harvard daga 1980 zuwa 1980 inda yayi karatu a kan zamantakewa.