Cécile Manorohanta
Cécile Manorohanta | |||
---|---|---|---|
18 Disamba 2009 - 20 Disamba 2009 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 20 century | ||
ƙasa | Madagaskar | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Jean Adolphe Dominique (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Cécile Manorohanta (Cécile Marie Ange Manorohanta) 'yar siyasa ce ‘yar kasar Madagascar wacce ke aiki a gwamnatin Madagascar a matsayin mataimakiyar Firayim Minista na cikin gida tun daga shekara ta 2009. A baya ta zamo Ministan Tsaro daga 2007 zuwa 2009.
An nada Manorohanta a mukamin ministan tsaro a ranar 27 ga Oktoba 2007 a gwamnatin Firayim Minista Charles Rabemananjara . Ita ce mace ta farko da ta zamo ministan tsaro a kasar ta.
A ranar 9 ga watan Fabrairun shekara ta 2009, Manorohanta ta sanar cewa zatayi murabus, tana mai cewa "bayan duk abin da ya faru, na yanke shawara a yanzu ba zan kasance cikin wannan gwamnati ba, " [1] tana nufin harbi na ranar 7 ga watan Fabira, a lokacin zanga-zangar Madagascar ta 2009, inda 'yan sanda suka harbe akalla masu zanga-zanga mutum 50. [2] An nada shugaban ma'aikatan soja Mamy Ranaivoniarivo don maye gurbin Manorohanta a wannan rana.[3]
A karkashin shugaban rikon kwarya Andry Rajoelina, an sake nada Manorohanta a mukamin siyasa matsayin Mataimakiyar Firayim Ministan Cikin Gida a ranar 8 ga Satumba 2009. [4][5]
A ranar 18 ga watan Disamban shekara ta 2009, Rajoelina ya sauke Firayim Minista Eugene Mangalaza, wanda bangarorin adawa suka amince da nadin a matsayin wani bangare na yarjejeniyar raba iko, kuma ya bayyana cewa zai nada Manorohanta a madadinsa. Duk da hakan, a ranar 20 ga Disamba 2009 Rajoelina a maimakon haka ya nada Albert Camille Vital a matsayin Firayim Minista.
Tun daga shekarar 2013 ta kasance shugabar Jami'ar Antsiranana .
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Madagascar defense minister resigns
- ↑ "Madagascar protesters shot dead". Al Jazeera. 2009-02-08. Retrieved 2009-02-08.
- ↑ "Defence minister quits over Madagascar bloodbath", AFP, 9 February 2009.
- ↑ "SADC 'rejects, condemns' new Madagascar govt", AFP, 8 September 2009.
- ↑ "Monja Roindefo; Un gouvernement de 31 membres", Madagascar Tribune, 9 September 2009 (in French).
Political offices | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |