Cavaline Nahimana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cavaline Nahimana
Rayuwa
Haihuwa 14 ga Janairu, 1997 (27 shekaru)
ƙasa Burundi
Sana'a
Sana'a long-distance runner (en) Fassara
Athletics
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Cavaline Nahimana (an haife ta a ranar 14 ga watan Janairu 1997) [1] 'yar tseren nesa ce (long distance runner) na Burundi. A cikin shekarar 2019, ta yi takara a cikin manyan tseren mata a Gasar Cin Kofin Ƙasa ta Duniya ta shekarar 2019 IAAF. [1] A shekarar 2019, ta kuma shiga gasar tseren mita 5000 na mata a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta shekarar 2019 da aka gudanar a Doha, Qatar. [2] Ba ta cancanci shiga wasan ƙarshe ba. [2]

A shekarar 2014, ta shiga gasar tseren mita 3000 na 'yan mata a gasar wasannin Olympics ta matasa ta lokacin zafi na shekarar 2014 da aka gudanar a birnin Nanjing na ƙasar Sin.

A shekarar 2017, ta fafata ne a gasar tseren manyan mata a gasar cin kofin duniya ta IAAF na shekarar 2017 da aka gudanar a birnin Kampala na ƙasar Uganda. [3] Ta ƙare a matsayi na 19. [3]

A shekarar 2019, ta wakilci Burundi a gasar cin kofin Afirka na shekarar 2019 da aka gudanar a Rabat, Morocco a gasar tseren mita 5000 na mata. [4] Ta ƙare a matsayi na 8. [4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Senior women's race" (PDF). 2019 IAAF World Cross Country Championships. Archived (PDF) from the original on 27 June 2020. Retrieved 27 June 2020.
  2. 2.0 2.1 "Women's 5000 metres - Heats" (PDF). 2019 World Athletics Championships. Archived (PDF) from the original on 3 October 2019. Retrieved 27 June 2020.
  3. 3.0 3.1 "Senior women's race" (PDF). 2017 IAAF World Cross Country Championships. Archived (PDF) from the original on 29 June 2020. Retrieved 29 June 2020.
  4. 4.0 4.1 "Women's 5,000 metres". 2019 African Games Results. Archived from the original on 20 September 2019. Retrieved 20 September 2019.