Jump to content

Charles Nkazamyampi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Charles Nkazamyampi
Rayuwa
Haihuwa Bujumbura, 1 Nuwamba, 1964 (60 shekaru)
ƙasa Burundi
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle da middle-distance runner (en) Fassara
Athletics
Sport disciplines 800 metres (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 
Tsayi 184 cm
Charles Nkazamyampi

Charles Nkazamyampi (an haife shi a watan 1ga watan Nuwambar shekarar 1964) ɗan wasan tseren matsakaicin zango ne daga kasar Burundi. Zakaran Afirka na 1992, ya kasa shiga gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarar 1992 saboda Burundi ba ta shiga ba. A shekarar 1993 ya ci lambar azurfa a tseren mita 800 a gasar cikin gida ta duniya, inda ya kare bayan Tom McKean. Daga baya Nkazamyampi ya fafata a gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarar 1996 ba tare da kai wasan karshe ba.[1]

Mafi kyawun lokacinsa na sama da mita 800 shine 1:44.24 mintuna, wanda aka samu a 1993.[2]

Ayyukan Bayan Sana'a

[gyara sashe | gyara masomin]

Charles shine wanda ya kirkiro 'Foundation Charles Nkazamyampi' (FCN), wanda ke amfani da wasanni don hada kan al'ummomi da inganta zaman lafiya a duk fadin kasar Burundi. Suna aiki a larduna 8 a fadin Burundi kuma suna karfafa matasa su sanya hannu kan alkawurran samar da zaman lafiya don kokarin dakile yiwuwar tashin hankali a nan gaba. [3]

1. ^ "Foundation CHarles Nkazamyampi" . 3 August 2021. Retrieved 3 August 2021. {{ cite web }} : |

first= missing |last= ( help )

  1. Foundation Charles Nkazamyampi
  2. Charles Nkazamyampi at World Athletics
  3. "Foundation CHarles Nkazamyampi" . 3 August 2021. Retrieved 3 August 2021. Empty citation (help) : | first= missing |last= ( help )